
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Borno ta tura jami’ai zuwa ƙauyen Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba bayan satar wasu ɗalibai da ba a tantance da adadinsu ba yayin da ake tsaka da rubuta jarrabawar NECO daga wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne.
Maharan, waɗanda ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun farmaki makarantar ne da misalin ƙarfe 9 na safe, inda suka riƙa harbe-harbe na kan-mai-uwa-da-wabi kana daga bisani suka yi awon-gaba da ɗalibai da matan da ke sayar da kayan abinci a farfajiyar makarantar, kamar yadda binciken farko ya nuna.
Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan, Nahum Daso ya bayyana cewa an yi ba-takashi tsakanin jami’an tsaro da maharan, lamarin da ya kare samun gagarumar nasarar garkuwar.
Haka ma, Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Adamawa, Adamu Fintiri akan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Mista Solomon Kwamagar, wanda shi ma ɗan Lassa ne, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a safiyar ranar Litinin.
A cewarsa, maharan sun garzaya yankin ne akan babura gabanin su kutsa cikin makarantar, inda suka halaka malami ɗaya da sace wasu ɗalibai.
Shugaban ƙungiyar haɗakar matasan Borno ta kudu, Samaila Kaigama, ya faɗa wa jaridar PUNCH Online cewa maharan sun je wajen ne cikin shiga irin ta sojoji da na kayan jami’an tsaron gandun daji.
A ranar 16 ga watan Mayu ne Blueprint.ng ta ruwaito cewa an sace ɗalibai guda 42 a wani harin da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar a makarantar firamare da ƙaramar sakandare da ke Mussa a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba.
Sanatan Borno ta kudu, Ali Ndume ya ce waɗanda aka sacen sun haɗa da ɗaliban Government Day Secondary School, ɗaliban firamare guda 28 da wasu yara 10 daga gidajensu.
