Boko Haram ta ba gwamnati kwana uku na amsa buƙatunta ko ta halaka mutane 416 da ta sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mayaƙan Boko Haram sun sake jefa fargaba acikin al’umma a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya yayin da suka ba wa hukumomi wa’adin kwanaki uku na makomar mutane guda 416 da suka sace, yayin da suke gargaɗi akan yunƙurin ceto su da ƙarfi.

A wani faifan bidiyo da mayaƙan ƙungiyar suka fitar a safiyar ranar Litinin, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa matuƙar aka gaza biyan buƙatun zuwa lokacin da ta bayar, za ta kai mata da yaran zuwa wasu ɓoyayyun wurare da ba za a sake ganin su ba.

‘Yan ta’addan, waɗanda suka yi shiga cikin kayan sojoji, sun bayyana cewa a shirye suke su yi yaƙi sannan suka ce suna maraba da dukkan wani yunƙuri daga gwamnatin Nijeriya na ceto mutanen, wanda ke nuna alamar sun shirya tunkarar dakarun tsaron Nijeriya.

Duk da wannan gargaɗi cikin harshen Hausa da Turanci, ƙungiyar ba ta bayyana takamaiman buƙatun nata ba.

Haka kuma, ta jaddada cewa da gaske take akan iƙirarin nata musamman wajen gargaɗi ga ƙungiyar haɗakar matasa ta kudancin Borno (BOSYA) da gwamnatin Nijeriya.

Da fari, rahotanni sun bayyana cewa, mayaƙan sun nemi a biya fansa Naira biliyan 5 a matsayin kuɗin fansar sako mutanen kamar yadda BOSYA ta bayyana.

By Babaji