Borno: Boko Haram sun yi garkuwa da sababbin mataimakin ciyaman da kansiloli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun yi awon-gaba da sabon zaɓaɓɓen mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno da wasu kansiloli biyu, ƙasa da kwana biyar da zaɓar su a zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a ranar Laraba akan hanyar Kamuya zuwa Buni-Yadi, wato wadda ta haɗa wasu yankunan jihohin Borno da Yobe, kuma ta shahara da fuskantar hare-hare da wasu munanan ayyuka.

Majiyoyi daga iyalan mataimakin ciyaman ɗin sun bayyana sunansa a matsayin Alhaji Sa’idu, sai kuma kansilolin waɗanda aka ce su ke wakiltar mazaɓun Zarawuyaku da Miringa.

An gano cewa, waɗanda al’amarin ya afka musu suna daga cikin fasinjojin da ke tafiya a wata motar Bos ƙirar Hizbah Hummer bayan tasowarsu daga Potiskum zuwa Biu, inda a yayin haka ne mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka tare su.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, wani ɗan gidansu da ya nemi a sakaye sunansa ya ce maharan sun tsayar da motar ne a tsakanin Kamuya da Buni-Yadi gabanin tilasta wa zaɓaɓɓun jami’an da wasu fasinjoji zuwa wani waje da ba a sani ba.

Tuni majiyar ta yi magiya ga gwamnatocin tarayya da na jihar tare da hukumomin tsaro da su gaggauta ƙaddamar da atisayen ceto mutanen da sauran waɗanda aka kama cikin aminci.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu saƙo na musamman daga rundunar ƴan sanda jihar ba duk da yunƙurin neman kakakinta, ASP Nahum Kenneth Daso da aka yi.

By Babaji