Buhari bai ɗauki ‘yancin ‘yan ƙasa da wasa ba – Malami

Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya jaddada ƙudurin gwamnatin Buhari na ci gaba da kare ‘yancin ‘yan ƙasa.

Haka nan, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasance mai martaba ‘yancin ‘yan ƙasa tun kafuwarta.

Malami ya bayyana haka ne wajen ƙaddamar da majalisar gudanarwa karo na biyar na Hukumar Kula da ‘Yancin Ɗan’adam ta Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce gwamnati na bin dokokin kare ‘yancin ɗan’adam sau da ƙafa, kuma ta biya haƙƙoƙin mutane kamar yadda aka buƙace a lokuta daban-daban.

A cewar Malami, gyaran da aka yi a 2010 ya bai wa hukumar damar gudanar da ayyukanta da kanta ba tare da kasancewa a ƙarƙashin ikon wani ko wasu ba.

Ya ci gaba da cewa an yi dukkan abin da ya dace game da hukumar ne domin ba ta damar bai wa gwamnati shawarwari kan harkokinta yadda ya kamata na kare ‘yancin ‘yan Nijeriya a gida da waje.

Tare da ba da misalin yadda gwamnati ta biya haƙƙin da ya hau kanta na ‘yan acaɓar da suka rasa rayukansu a Apo 2012 ta dalilin jami’an tsaro da sauransu.