Buhari ya ƙaddamar da sabon kamfanin NNPC bayan sauya masa fasali

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da sabon Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPC Limited), wanda hakan ya sauya wa kamfanin fasalin gudanarwa daga ƙarƙashin gwamnati zuwa ƙarƙashin ‘yan kasuwa wanda zai ci gaba da gudana ta hanyar hannun jari.

Wannan na nufin kamfani NNPC Limited zai ci gaba da gudana ne a matsayin mai zaman kansa amma ba na gwamnati ba kamar yadda aka sani.

Da yake jawabi yayin taron ƙaddamarwar Shugaba Buhari ya ce, “Mun sauya fasalin kamfanin fetur ɗinmu ne a yau 19 ga Yulin 2022 domin ƙarfafa shi.

“Daga yanzu NNPC Limited zai riƙa aiki ne a matsayin kamfanin mai na ‘yan kasuwa wanda ke da masu hannun jari jajirtattu a cikinsa sama da miliyan 200.”

Ƙaddamar da sabon NNPC ɗin a hukumance na zuwa ne bayan da aka kammala sauya fasalin gudanarwarsa zuwa wanda haɗakar kamfanoni abokan hulɗarsa za su ci gaba da jan ragamarsa.

Dokar da ta sahale sauya fasalin kamfanin ya soma aiki ne tun a ranar 1 ga Yuli.

By Editor