Mata 1,000 za su samu bashi domin dogaro da kai a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato da haɗin gwiwar Bankin Sterling, za su bada bashin ga mata 1,000 masu qananun sana’o’i a Sakkwato da suka fito daga gundumomi, wasu  Masallatan Juma’a 50, da ƙungiyoyin addinin Musulunci 50, tare da sake kira ga jama’ar jihar nan da su duƙufa a cikin ƙanana da matsakaitan sana’o’i domin samun kuɗaɗen lalurar yau da kullun su da iyalansu.

Shugaban zantarwar hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ne ya yi wannan kiran yayin da yake buɗe taron wayar da kai a kan bashi marar ruwa wanda bankinSterling sashen Musulunci da hukumarsa suka shiryawa uwayen ƙasa, masallatai da ƙungiyoyin addinin Musulunci.

Ya ƙara da cewa taron wayar da kan na da manufar tallafa wa masu rauni a ciki waɗanda ke son kafa ƙananan sana’o’i samun bashin ƙarƙashin haɗakar dake akwai tsakanin hukumarsa da bankin na  Sterling ɓangaren Musulunci. 

Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ƙara da cewa hukumarsa ta damu matuqa da yanayin tsadar rayuwa, matsalolin tsaro da yanayin talauci da suka addabi jama’a musamman mazauna karkara.

Kimanin mutum dubu ne za a fara shirin da su bayan an tantance su kuma sun cika sharuɗɗan da aka shata kuma gundumomi, masallatai kana da ƙungiyoyin addini ne za su samar da mutum dubu, inji shi.

Da take gabatar da jawabi yayin taron, Manajar bankin Hajiya Nafisa Umar ta bayyana sharuɗɗa da ƙa’idojin samun bashin maras riba. 

Daga nan ta yi kira ga mahalarta da su jajirce domin ganin al’ummarsu sun amfana da wannan damar.

Hajiya Nafisa ta yi godiya ga hukumar zakka akan qulla wannan haɗaka da bankinsu.

Wasu da suka magantu a lokacin taron sun haɗa da shugaba da sakataren kwamitin haɗakar Hajiya Kula Ahmad da Aminu Bello Isah.

Taron an shirya shi  ga uwayen koasa 27, masallaci 50 ƙungiyoyin addini 50 kuma ya samu halartar, Alƙalin Malamman Sakkwato, uwayen ƙasa da  malaman makaratun gaba da sakandare, ‘yan jarida da sauransu.