Buhari ya taya ɗan uwansa, amininsa Mamman Daura, murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeyiya Muhammadu Buhari ya taya Malam Mamman Daura murna cikar sa shekaru 82 da haihuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, 2021.

Cikin saƙon shugaban ga ɗan uwan nasa kuma mafi kusanci da shi, wanda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya sanya wa hannu a Abuja, Shugaba Buhari ya ce, “babu wanda ya fi dacewa da na taya shi murnar zagowar ranar haihuwa, kamar Malam Mamman Daura.”

Sannan ya bayyana shi a matsayin “mutum mai cikar nagarta, wanda da dama ake mutuntawa kan yadda ya nemi ilimi kuma ya ke da cikakken hankali da sanin yakamata, sa’annan ya yi fice gurin kafewa kan aikata daidai.

“Allah ya Albarkace ka da ƙoshin lafiya da walwala, don cigaba da aiki ga ƙasa. Ka cigaba da kasancewa cikin halin lafiya, don yawaita aiki ga ƙasa. Allah ya albarkace ka da tsawon rayuwa cikin ƙoshin lafiya.”

A Nijeriya dai, a na kallon Malam Mamman Daura a matsayin mafi faɗa a ji a gwamnatin Shugaba Buhari.