Buri na Jihar Nasarawa ta kasance mafi tsafta a ƙasar nan – Hon. Margret Elayo

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Sabuwar kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa na gwamnatin jihar Nasarawa Honorabul Margret Elayo tace babban burin ta shine ta tabbatar jihar ta Nasarawa ta cigaba da kasance cikin tsaftataccen yanayi har ma ta fi kowacce jiha a fannin.

Honorabul Margret Elayo ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu a sabon ofishin nata dake ma’aikatar a birnin Lafiya babbar fadar jihar a mako da ake ciki game da yadda za ta gudanar da harkokin ma’aikatar da sauransu.

A kan haka nema acewarta tun da ta kama aiki a matsayin sabuwar kwamishiniyar ma’aikatar take ta yin duka mai yuwa musamman ta ganawa da hukumomi da suka dace ciki har da ma’aikatan ma’aikatar baki daya dangane da bukatar aiki tukuru don tabbatar da cimma burin akarshe.

Ta ce tabbas kowanna al’umma takan samun kima da daraja a idon duniya ne sakamakon yanayin tsaftar muhallin ta akoyaushe inda ta kuma yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnatin sa musamman ta wannan aikin kwasar shara da ake gudanar a jihar baki daya akowanna karshen wata inda tace tabbas kawo yanzu shirin na cigaba da aifar da ƙa mai ido.

Kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasar ta gwamnatin jihar Nasarawa honorabul Margret Elayo ta kuma sha alwashin tabbatar da ita da duka sauran ma’aikatan zasu riga gudanar da shugabanci da mitsali don acewar ta dukansu zasu rika fito suma suma fafata a cikin aikin shara da kuma kwashe magudanun ruwa da suka toshe da sauran su don karfafawa al’umma baki ɗaya gwiwa.

Dangane da batun asarar dukiyoyi da rayuka da a wasu lokutan akan samu sakamakon tsawalewar kasa wato erosion a turance bayan ruwan sama a jihar honorabul Margret Elayo ta bayyana cewa tuni take ta tuntubar hukumomi da cibiyoyi da suka dace da nufin samo mafita ga mumunar lamarin sa’anan suna cigaba da tattauna yadda za a cigaba da agaza wa wadanda lamarin ke shafa da sauran su inji ta kana ta kuma yaba wa kokarin gwamnatin gwamna Abdullahi Sule a wannan fanni ta ma’aikatar.

A ƙarshe sai sabuwar kwamishiniyar Margret Elayo ta nanata kiran ta na musamman zuwa ga al’ummar jihar baki daya ciki harda wadanda ke yankunar karkara kada su karaya su cigaba da bai wa ma’aikatar cikakken gudumawa a kokari da suke yi na tsaptace duka muhallin jihar da sauran nauyi dake wuyar su inda ta kara da cewa ma’aikatar bazata iya yin komai ba batareda gudunmawar da haɗin kansu ba.

 .

By ukarofi