Majalisa ta yi watsi da ƙudurin dokar mulkin karɓa-karɓa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Wakilai ta yi watsi da ƙudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karɓa-karɓa a tsarin shugabancin Nijeriya.

Kudurin dokar na neman yi wa kundin tsarin mulki na 1999 gyaran fuska domin ba da damar yin karɓa-karɓar kujerar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a tsakanin yankunan siyasar Nijeriya guda 10.

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Okezie Kalu ne ya gabatar da kudurin, wanda ke cikin jerin sauye-sauye bakwai a kundin tsarin mulki da majalisar ta tattauna a kansu a zamanta na ranar Talata.

Bayan gabatar da kudurin a zaman da Kalu ya jagoranta, Honorabul Aliyu Madaki (NNPP, Kano), ya soki ƙudurin da cewa tsarin raba-daidai na kasa ya riga ya magance duk abubuwan da ƙudurin ke nema.

Aliyu Madaki ya ci gaba da cewa batun karɓa-karɓa, abu ne da ya kamata a bar wa jam’iyyun siyasa su tsara wa kansu idan sun ga dama, amma babu bukatar mayar da shi doka a cikin kundin tsarin mulki.

Amma a martaninsa, Honorabul Ali Isah (PDP, Gombe) ya bayyana cewa yin dokar mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin zai tabbatar da adalci ta yadda kowane yankin kasar zai ji cewa ana damawa da shi, ba a mayar da shi saniyar ware ba.

Sai dai kuma, Honorabul Sada Soli (APC, Katsina) ya bayyana cewa “kudurin zai yi mummunar illa ga hadin kan kasar nan,” Ya kara da cewa karba-karba zai takaita zabin da al’ummar Nijeriya ke da shi kuma zai iya jefa kasar a hannun marasa kwarewa.

Amma Honorabul Kalu, wanda ya jagoranci zaman na ranar Talata, ya mayar da martani da cewa kowane yanki a kasar yana da mutanen da ke da gogewar da za su iya shugabantar kasar cikin kwarewa.

Ya bayyana cewa manufar ƙudurin nasa ita ce samar da tsarin da zai ba da cikakkiyar damar yin shugabanci ga kowane shiyya a kasar, ta yadda za ta ba da gudummawarta wajen kawo ci-gaba.

Sai dai kuma Honorabul Shina Oyedeji ya kalubalance shi da cewa, manufar tsarin dimokuraɗiyya ita ce bayar da cikakkiyar damar yin gasa mai tsafta, saboda haka, yin dokar mulkin karba-karba ya ci karo da manufar dimokuradiyya.

Ya ce, don haka, “Ya kamata a ba wa kowa damar yin takara a kowane mataki da kuma lokaci.”

Shi ma Honorabul Bello El-Rufai (APC, Kaduna) a yayin da yake fatali da kudurin, ya bayyana cewa yin dokar mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Nijeriya, babu abin da zai haifar sai kiyayya ta ƙabilanci, duba da yawan al’ummomin da ke ƙasar.

Bayan sauraron ɓangarorin da suka tafka muhawarar, Mataimakin Shugaban Majalisar ya sa a yi kuri’a ta hanyar murya a zauren majalisar, inda masu adawa da kudurin suka samu rinjaye.

By ukarofi