Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ɗankaka Husaini Bebeji mai bai wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf shawara a ofishin mataimakin Gwamna ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano a yadda ake tafiyar da gwamnati sai sambarka.
Ya ce Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya fitar da su kunya kuma yana kan fitar da su domin abinda suka gayawa talakawa su zaɓe shi za a yi musu su ake yi idan aka tsaya aka duba mutumin da ke cikin birni yanzu ba zai maganar hanya ba domin ana yin sabbin da gyara wasu haka ana baiwa ilimi kulawa sosai da ƙoƙarin samar da ruwa domin ya wadata a ko’ina birni da karkara duk da gwamnati ba ta wuce shekara biyu ba, amma babu inda ba a taɓa anyi aiki ba babu inda ba su san an yi zaɓe ba.
Alhaji Ɗankaka Husaini Bebeji ya ce game da batun maganganu da ake yawo da shi na siyasa a ce wannan zai koma wata jam’iyya duk ana yi ne don a hana masu aiki su yi wa mutane aiki domin ba a zo maganar siyasa ba ma, bai dace ma a yi shi yanzu kwata- kwata. A tsari na Damakwaraɗiyya bai kamata shekara biyu ma bata cika ba ,azo ana harin gobe kuma Allah ne yasan da goben, zaka kai ko ba zaka kai ba, an zo ana bazama mutane ana ɓarnar kuɗi don kawai goben da ba a san me za ta zama ba.
“Mu Gwamnan mu na jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a natse yake babu maganar gobe a wajensa yau muke yi gobe ko ta Allah ce kuma da yardar Allah Abba sai ya zama zakara a duk fadin Kasar nan mu burin mu talakawa su san ana yi musu kuma suna ji shi yasa yake ta samun lambobin karramawa kan ayyukan da yake,” inji ɗankaka.
Ya ce a cikin ayyukan da za su yi wa al’umma a cikin kashi 100 yanzu an yi kashi 69 wannan kuma a shekara ta uku da zata zo za su cike. Da yarda Allah a jihar Kano bayan sun mayar da kwaryar Birnin Kano ƙasaitaccen alƙarya na zamani dukkan ƙananan hukumomi na karkara da ƙauyukansu sai sun gamesu da hanyoyi da gadoji da za a shiga za a fita.
Alhaji Ɗankaka Husaini Bebeji yace a wannan mulki da ake na Abba Kabir Yusuf babu abinda al’ummar jihar Kano zasu ce sai godiya ga Allah sun san abinda ake an sami zaman lafiya ana buɗe makarantu ilimi ilmi na bunƙasa ana tallafawa cigaban al’umma maza da mata daga wannan lokaci Kano ta tashi kenan za ta riƙa cigaba ba za a kuma cewa ta gaza ba, zamu zama ta dabo sha yabo, tumbin Giwa ko da mai kazo an fika, wannan kirarin shine zai tabbata a wannan gwamnatin.
