Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Shugaban ƙungiyar cigaban al’ummar ƙabilar Bassa dake ƙaramar Hukumar Toto a jihar Nasarawa, Mista Emmanuel Gbaji ya ce a yanzu haka al’ummar sa na ƙabilar Bassa dake yankin sun koma ainihin gidajensu na gado don cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba bayan wani mummunar rikicin ƙabilanci da ya ƙi ci ya kuma ƙi cinyewa a kwanakin baya a yankin tsakanin su da wasu ƙabilun da daɗewa.
Mista Emmanuel Gbaji ya sanar da haka ne a jawabinsa a wajen wani muhimmin taron shugabannin al’ummomi daban-daban wadda aka gudanar ranar Litinin na makon da ake ciki a ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin gargajiya dake Lafiya fadar gwamnatin jihar.
Shugaban al’ummar Bassa Mista Emmanuel Gbaji ya ce ba shakka dole al’ummarsa su cigaba da yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule da hukumomin tsaro daban-daban dake jihar musamman waɗanda ke yankin da shugaban ƙaramar hukumar Toto da shi ma wadda ya kiro taron tattaunawar wato wani ɗan siyasa mai taimakawa gwamnan jihar akan harkokin yawon buɗe ido da gargajiya mai suna Honorabul Solomain Tablue Peɓkya dangane da aikin sulhu na tuƙuru da suka ta yi har a ƙarshe aka shawo kan rikicin al’ummarsa kuma suka samu damar komawa gidajen nasu na asali.
Ya ce tabbas wannan taron shugabannin al’ummomin dabandaban yana aifar da da mai ido kana ya yi kira a daure da shi don samun zaman lafiya mai dawama a yankin nasu na Toto dama jihar bakiɗaya.
Tun farko a jawabin sa na maraba wanda ya shirya zaman tattaunawar Honorabul Solomon Tablue Peɓkya bayan godewa duka shugabannin da suka halarci taron zaman lafiyar musamman waɗanda suka fito daga yankunan karkara a jihar ya nanata musu cewa zaman gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ne yaga yadace a rika yi akowanna shekara inda ya buƙace shi ya kira duka shugabannin al’ummar a duka matakai suzo su hadu su tattauna akan batutuwan tsaro dake damunsu a yankunan nasu da yadda za a samo mafita da sauran su.
Honorabul Solomain Tablue Peɓkya yace tabbas idan anason samun zaman lafiya daya dace a jihar dole ne kowa daga kowanna kabila yazo a hadu a kuma bar maganar kabilanci da addini a riƙa klƙaunar juna ta haka ne kawai za a iya cimma burin.
Daga nan ya sake yaba wa ƙoƙarin gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule musamman akan batutuwa da suka shafi tsaron jihar bakiɗaya inda ya ce kawo yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin ƙasar nan inda ake samun dawamamman zaman lafiya sakamakon shirye-shiryen gwamnatin nasa na musamman da kuma zama da yake yi shi kansa akai-akai da duka bangarori dake rikici da juna inda a ƙarshe a sasantasu da sauran su kana ya buƙaci duka shuganannin su tabbatar sun isar da saƙon lafiyar wa jama’ar su bayan sun koma gida.
A nasu ɓangaren mahallata taron wato shugabannin al’ummomi dabandaban dake fadin jihar duk sun yaba wa honorabul Solomon Tablue Peɓkya dangane da hangan nesa da yayi na kira taron inda duk suka yi jawabi daya bayan daya akan yanayin tsaro a yankunan nasu da kuma wasu nasarori da suka samu kawo yanzu waje dakile matsalolin tare da kira ga gwamnatoti a duka matakai su kara himma wajen tabbatar da cikakken tsaro a fadin jihar baki daya.
Honorabul Solomon Tablue Pevkya dai ya kasance na hannun damar gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule inda sau dayawa shi gwamnan kan yi amfani da shine wajen hada tarurrukan zaman lafiyar kamar wannan da sauran su a fadin jihar bakiɗaya.
