Burin ƙasar Sin shi ne “a gudu tare a tsira tare”

Spread the love

Daga SAMINU HASSAN

Yayin da ake ci gaba da gudanar da taron ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G20, a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia, hankula na karkata ga ganawar da manyan jami’an sassan ƙasashe daban daban, mahalarta taron za su gudanar.

Cikin irin waɗannan ganawa, akwai wadda aka tsara gudanar ta tsakanin ministan wajen ƙasar Sin Wang Yi, da sakataren wajen Amurka Antony Blinken, a gefen taron mai matuƙar muhimmanci.

Masharhanta dai na ganin idan har ana son cimma gajiya daga ganawar sassan biyu, to ya zama wajibi ɓangaren Amurka ya nuna sahihanci, da yin magana ɗaya, ta yadda hakan zai haifar da amincewar juna, da kyautata alaƙar kasashen 2 yadda ya kamata.

Duk da cewa an kafa ƙungiyar G20 ne da nufin warware manyan matsalolin tattalin arzikin duniya, kamar daidaita yanayin hada hadar kuɗaɗe, da daƙile sauyin yanayi, da wanzar da ci gaban duniya mai ɗorewa. A bangaren Sin da Amurka, akwai ƙarin batutuwa da ya wajaba sassan 2 su ƙara maida hankali a kan su, musamman ma batun sabanin su game da kare ikon mulkin kai, da tsaro, da harkokin kasuwanci, da kyautata diflomasiyya.

Har kullum, manufar ƙasar Sin ba ta sauyawa, game da burinta na ganin sassan duniya sun yi tafiya tare, domin cimma moriyar juna, da samar da al’ummar duniya mai makomar bai ɗaya ga dukkanin bil adama.

A wannan gaba, fatan da yawa daga masu fashin baki, shi ne yayin ganawar kai tsaye ta wadannan manyan jami’ai biyu, ɓangaren Amurka zai amince da muradun ƙasar Sin, na ƙaurace wa tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, musamman ma batun yankin Taiwan, wanda a baya bayan nan Amurkan ke ta aiwatar da wasu matakai, waɗanda ba za su haifar da da mai ido ba.

Cikin irin waɗannan matakai akwai batun ƙarfafa ayyukan sojinta, da na tattalin arziki, da kawance da ƙasashen gabashin Asiya, a wani yunƙuri na abun da take kira “Daƙile faɗaɗar tasirin ƙasar Sin”.

Don haka dai ana iya cewa, dangantaka tsakanin Amurka da Sin a wannan lokaci, na cikin wani yanayi mai sarkakiya. Duk da cewa jami’an sassan biyu na ganawa, da tattaunawa sa’i sa’i. Burin kowa a yanzu, bai wuce ganin manyan ƙasashen 2 sun fahimci juna ba. Kana su ƙaurace wa dukkanin wani nau’i na fito na fito, tare da rungumar matakan da za su amfani al’ummun su da duniya baki ɗaya.

By Editor