CBN ya bayyana hanyoyin kare kai daga ’yan damfara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi kira ga duk masu hulɗa da bankuna a ƙasar da su kare bayanan kuɗinsu ta hanyar guje wa raba lambar sirri (PIN), kalmomin shiga da sauran bayanan banki masu muhimmanci da kowa, ko wane ne.

Bankin ya fitar da wannan gargaɗi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na hukuma na ɗ (tsohon Twitter), a matsayin wani ɓangare na bikin makon wayar da kan jama’a kan kuɗi na duniya na shekarar 2026, wato Global Money Week.

A cewar CBN, wannan faɗakarwa ta zama dole ne sakamakon ƙaruwar damfara da yaudara da ake yi wa masu hulɗa da bankuna, musamman wazanda ba su yi zato ba. Bankin ya buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri a kowane lokaci, tare da tabbatar da cewa bayanansu na banki suna nan a ɓoye kuma ba su fito fili ba.

CBN ya jaddada cewa bai kamata kwastomomi su bayyana muhimman bayanansu na kuɗi ga kowa ba, ko da mutum ya ce shi ma’aikacin banki ne. A cewar bankin, kariyar bayanai ita ce mafi ingancin hanya ta hana satar kuɗi da damfara.

“Ku kare kuɗinku ta hanyar kare bayananku. Yayin da muke bikin Global Money Week 2026, ku tuna cewa PIN, kalmomin shiga da bayanan bankinku ba su kamata ku ba kowa ba — ko da ya ce yana aiki da bankinku. Ku kasance masu lura. Ku kasance cikin aminci,” inji sanarwar bankin.

Gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar damfara inda masu aikata laifi ke kwaikwayon jami’an banki domin yaudarar mutane su ba su bayanan sirri. Sau da yawa masu damfara kan tuntuɓi jama’a ta waya, saƙonnin tes, imel ko kafafen sada zumunta, suna ƙaryar cewa su wakilan cibiyoyin kuɗi ne.

Da zarar mutum ya fallasa bayanansa, masu damfara kan samu damar shiga asusunsa ba tare da izini ba, su gudanar da mu’amaloli na satar kuɗi. Masana harkokin kuɗi sun sha nanata cewa irin waɗannan dabarun damfara sun ƙara ƙwarewa a zamanin nan, wanda ke sa wayar da kan jama’a ta zama muhimmin makami wajen yaƙi da laifukan kuɗi.

Makon Global Money Week wani shiri ne na duniya da ake gudanarwa duk shekara domin inganta ilimin sarrafa kuɗi, ɗabi’ar amfani da kuɗi cikin hikima da kuma kare masu amfani da harkokin kuɗi. Ana gudanar da shi a ƙasashe da dama ciki har da Nijeriya ta hanyar shirye-shiryen wayar da kai, musamman ga matasa, domin su koyi yadda za su kare kansu daga yaudara da cin zarafi.

Masu shirya shirin sun bayyana cewa manufarsa ita ce ba mutane ilimi da ƙwarewar da za ta ba su damar yanke shawara mai kyau kan kuɗinsu, tare da kare kansu daga damfara da asarar dukiya.

By ukarofi