Hauhawar farashi ya ragu a Nijeriya – NBS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu zuwa kashi 15.06 cikin ɗari a watan Fabrairu 2026, daga kashi 15.10 da aka samu a watan Janairu.

Rahoton duba farashi na CPI na watan Fabrairu da hukumar ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa hauhawar farashin gaba ɗaya ta sauka da kaso 0.04 cikin zari idan aka kwatanta daga wata zuwa wata.

Wannan na nuni da cewa ƙaruwar farashin kayayyaki na ci gaba da raguwa a hankali, duk da cewa matsin tattalin arziki na nan.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashin abinci ta ƙaru zuwa kashi 12.12 cikin ɗari a Fabrairu, idan aka kwatanta da kashi 8.89 na watan da ya gabata. Wannan na nuna cewa duk da raguwar hauhawar farashi gaba ɗaya, farashin kayan abinci — wanda shi ne mafi tasiri ga rayuwar talakawa — har yanzu yana ƙaruwa.

A cewar NBS, a watan Fabrairu 2026 hauhawar farashin gaba ɗaya ta tsaya a kashi 15.06 cikin dari, ƙasa da kashi 15.10 na Janairu 2026. Amma idan aka duba daga wata zuwa wata, hauhawar farashin ta kai kashi 2.01 cikin ɗari, wanda ya fi na Janairu — wanda ya kasance ƙasa da sifili (-2.88%) — da kaso 4.89. Wannan yana nufin cewa matsakaicin farashin kayayyaki ya tashi cikin sauri a Fabrairu fiye da yadda ya tashi a Janairu.

Tun da farko, Kamfanin Nazarin Tattalin Arziki (FDC) ya yi hasashen cewa hauhawar farashin Fabrairu za ta sauka zuwa kashi 14.07 cikin ɗari, amma alƙaluman da aka fitar sun nuna adadin ya ɗan fi hakan.

Tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a shekarar 2023, farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zaɓi, lamarin da ya sa tsadar rayuwa ta yi muni ga yawancin ‘yan Nijeriya. Duk da cewa gwamnati ta ce farashin kayayyaki na fara sauka a ‘yan watannin nan, masu adawa da ita na cewa sauyin na bayyana ne kawai a takardu, ba a rayuwar jama’a ba.

Sabbin alƙaluman NBS sun sake janyo muhawara kan ko gaske ne tsadar rayuwa na raguwa, musamman ganin yadda farashin abinci ke ci gaba da hauhawa a kasuwanni da dama a faɗin ƙasar.

By ukarofi