Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna da sauran hukumomin da ke fitar da katunan biyan kuɗi su faɗaɗa yawan na’urorin cire kuɗi ta ATM a faɗin ƙasa, inda ya tanadi cewa nan da shekarar 2028 dole ne a samu aƙalla na’urar ATM ɗaya ga kowane katin biyan kuɗi 7,500 da aka fitar.
Sabon umarnin na kunshe ne cikin dokokin gudanar da na’urorin ATM a Nijeriya da CBN ta fitar, wanda ke nufin rage cunkoso, dogayen layuka da kuma matsalolin samun kuɗi a bankuna, musamman a manyan birane da yankunan karkara.
A cewar dokar, dukkan hukumomin da ke fitar da katunan biyan kuɗi — ciki har da bankuna, kamfanonin kuɗi da masu samar da ayyukan biyan kuɗi — dole ne su tabbatar da cewa sun tanadi isassun na’urorin ATM da za su iya biyan buƙatar abokan hulɗarsu. Wannan mataki na daga cikin kokarin inganta tsarin biyan kuɗi na zamani da kuma rage matsin lamba a rassan bankuna.
Umarnin ya fito ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 13 ga Maris, 2026, wadda Daraktan Sashen Manufofin Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Musa I. Jimoh, ya sanya wa hannu. An aike da sanarwar ga bankuna, cibiyoyin kuɗi da kuma masu samar da ayyukan biyan kuɗi domin su fara shiri tun yanzu kafin wa’adin 2028.
Masana harkar kuɗi na ganin cewa matakin zai taimaka wajen inganta samun kuɗi cikin sauƙi, ƙarfafa hada-hadar kuɗi ba tare da wahala ba, tare da rage matsalolin da ke tasowa sakamakon ƙarancin ATM a wasu yankuna. Haka kuma, ana sa ran zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar ƙarfafa amfanin hanyoyin biyan kuɗi na zamani a tsakanin al’umma.
Sai dai ana kuma hasashen cewa bankuna za su fuskanci ƙarin nauyin kuɗi wajen sayo, girkawa da kuma kula da sabbin na’urorin, musamman a yankunan da ba su da ingantaccen wutar lantarki da tsaro. Duk da haka, CBN na ganin cewa amfanin da jama’a za su samu ya fi duk wani ƙalubale na aiwatar da shirin.
