CBN ya cire takunkumi a asusun banki na Dala, ya mayar da shi $10,000 kullum

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya cire takunkumin da ya sa a asusun bankin Dala. Inda ya lara kuɗin da za a iya zubawa zuwa Dalar Amurka $10,000 a kullum.

Wannan bayani yana ƙunshe a wani jawabi da aka wallafa bayan ganawa da kwamiitin ma’aikatan banki a ranar Lahadin da ta gabata. 18 ga Yuni, 2023.

An shirya taron ne saboda niyyar samar da sababbin dokoki da za a ƙaddamar a harkar bankin.

Sabuwar dokar ta soke iyakar da aka sanya a kan hada-hadar asusun banki na Dala a shekarar 2021. Don yin biyayya ga wani umarni da CBN ta bayar.

A ‘yan kwanankin da suka wuce, kasuwar canji ta Nijeriya (FX) ta samu sababbin tsare-tsare waɗanda aka ƙaddamar mata don yin garambawul ga harkar tattalin arzikin ƙasar.

Idan ba a manta ba kuma a ranar 14 ga Yuni 2023, aka ba da sanarwar ba da farashi na bai ɗaya ga dukkan kasuwar canji ta Nijeriya da kuma karya farashin Naira.

CBN ta bayyana cewa, an yi wannan doka ne don kau da muna-muna da sauƙaƙa harkar canza kuɗin. Kuma hakan ne zai ciyar da kasuwar canjin gaba.