CBN ya soke lasisin bankin Heritage

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya ce ya ƙwace lasisin gudanar da aiki na bankin Heritage da ke ƙasar.A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce ya ɗauki matakin ne “domin tabbatar da ingantaccen tsarin kuɗi a ƙasar, kuma ya yi hakan ne a ƙarqashin sashe na 12 na dokar bankuna da sauran harkokin kuɗi (BOFIA) ta 2020”.

Babban Bankin ya ce, soke lasisin ya zama wajibi bayan da bankin na Heritage ya cigaba da saɓawa sashe na 12 (1) na BOFIA 2020 da gazawarsa wajen inganta ayyukansa na kuɗi inda yake haifar da babbar barazana ga daidaiton kuɗi.Hakan ya biyo bayan wata ganawa da CBN ya yi da bankin tare da tsara matakan sa ido daban-daban da nufin daƙile koma bayan tattalin arziki amma kuma bankin ya ci gaba da taɓarɓarewar kuma ba shi da wata alama ta murmurewa abin da ya sa CBN ya ɗauki matakin soke lasisin a matsayin mataki na gaba.

Haka zalika, CBN ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa ƙwarin gwiwar jama’a kan tsarin banki da kuma tabbatar da cewa ba a tauye tsarin hada-hadar kuɗin jama’a ba.Yanzu hukumar Inshorar kuɗi ta Nijeriya wato NDIC, ta karɓi ragamar gudanar da harkokin bankin na Heritage.

A ɗaya ɓangaren kuma, Babban bankin ya musanta shirin ƙwace lasisin Bankin Unity, Bankin Polaris da Bankin Keystone.Rahotanni na yanar gizo sun yi ikirarin cewa babban bankin zai soke lasisin bankunan uku, bayan soke lasisin bankin Heritage.Sai dai babban bankin na CBN ya ƙaryata wannan ikirari a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana cewa “ba shi da shirin yin hakan”.”Abin da ke ciki ƙarya ne, domin CBN ba shi da shirin yin hakan,” inji saƙon.

By ukarofi