Cire tallafin fetur: Gwamnatocin jihohi za su iya biyan mafi ƙarancin albashi, inji Falana

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yawan shiga yajin aikin ƙungiyoyin qwadago, Femi Falana (SAN) ya ce babu wata jiha da za ta ce ba za ta iya biyan mafi ƙarancin albashi ba biyo bayan cire tallafin da Gwamnatin Tarayya ta yi.Ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV Brief, inda ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta iya hana ‘yan ƙwadago shiga yajin aiki ba.”Babu wata jiha a Nijeriya a yau da ba za ta iya biyan fiye da mafi qarancin albashi ba saboda gwamnati ta cire tallafin man fetur a shekarar da ta gabata kuma shugaba Tinubu ya shaidawa ‘yan Nijeriya cewa za a yi amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin,” in ji Falana.“Duk gwamnatin jihar da ba ta biya mafi ƙarancin albashi na ƙasa ba, mu lauyoyi ba za mu bari ba, za mu kai ta kotu.“Za mu tabbatar da bin doka da oda, ciki har da cewa za mu shiga kotu domin ta ba da umarni, za a cire haƙƙin ma’aikata duk wata daga majiyar da ke Abuja.

Ba za mu lamunci haka ba.”A yayin shirin, lauyan kare haƙƙin ɗan Adam ɗin ya buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya, da ya sanya ido kan jihohin da suka gaza biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 a halin yanzu.Ya ce tun da biyan mafi ƙarancin albashi yarjejeniya ce da aka ƙulla cikin ‘yanci, gwamnatocin jihohin da ba su iya mutunta wannan yarjejeniya sun taka doka.“Da zarar an ƙulla sabuwar yarjejeniya, sabon mafi qarancin albashi ya zama dokar ƙasa. Gwamnatin tarayya tana da haƙƙi, kuma babban lauyan ƙasar yana da alhakin jan duk wata gwamnatin jiha da ba ta aiwatar ba zuwa kotu.”Ina nufin, babban lauyan gwamnati zai iya shigar da wata sabuwar ƙara, wanda hakan wani ci gaba ne mai kyau, da ya ce tsawon shekaru, mun zargi gwamnatocin jihohi da karkatar da haƙƙin ƙananan hukumomi,” inji shi.

Falana ya kuma ce za a tilastawa gwamnatocin jihohi su biya mafi ƙarancin albashi, domin ana cirewa daga majiyar ƙasa.

By ukarofi