CDOWA za ta horar da jami’ai mata don ƙarfafa su a kan tsaro

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Ƙungiyar matan jami’an Sibil defens civil defence officers wife Association (CDOWA) ta Jihar Gombe, ƙarƙashin hukumar tsaro ta ƙasa (NSCDC), ta shirya haɗa kai da ma’aikatar harkokin mata ta jihar domin ƙarfafa mata da kuma wayar da kan jama’a kan batutuwan tsaro.

Wannan shirin ya fito fili ne a yayin ziyarar ban girma da tawagar CDOWA ƙarƙashin jagorancin shugabar ta na jihar, Hajiya Hauwa Abdulmumin Muntaz, ta kai wa kwamishinar harkokin mata, Asma’u Iganus.

A lokacin ziyarar, jami’ar hulɗa da jama’a ta kungiyar, DSC Dorcas Dogara, ta bayyana sabon shirin da ake kira “Gallant Women Drivers” (GWD).

Tace Wannan shiri zai bai wa mata horo na musamman kan yadda za su ƙware a harkar tuƙi, tare da koya musu ilimin diflomasiyyar tsaro da hanyoyin kare lafiyar jama’a.

Ta ce, manufar shirin ita ce ƙara wa mata ƙarfin gwiwa, buɗe musu damar samun ayyukan yi a fannin sufuri da tsaro, da kuma taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta tsaron al’umma.

A nata jawabin, kwamishinar mata Asma’u Iganus ta yi maraba da shirin, inda ta kira shi “maɓuɗin canji” ga mata a jihar.

Asma’u Iganus, ta yi alƙawarin bayar da cikakken goyon bayan ma’aikatar ta tare da haɗa ƙungiyar da masu ruwa da tsaki da za su iya samar da tallafi da ƙwarewar fasaha domin ganin an cimma nasara.

By ukarofi