
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar yau Lahadi ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta sanar da naɗa Xabi Alonso a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta.
Ƙungiyar ta Turai ta bayyana haka ne ta shafinta na intanet.
Hakan na zuwa ne bayan cimma yarjejeniya a tsakaninta da Alonso akan zama mai horar da ‘yan wasan nata na tsawon shekaru huɗu, kamar yadda wani rahoto daga David Ornstein ya bayyana.
Ɗan ƙasar Sifaniyar zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yuli, 2026 a Stamford Bridge.
Bayan ganawa a lokuta da dama kocin mai shekaru 44, zai gaji Liam Rosenior da aka sallama a Afrilu ne a muƙamin.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Chelsea ke neman sabon salo da kwanciyar hankali bayan shekaru na sauye-sauyen koci-koci da kuma rashin daidaito a sakamakon wasanni.
Xabi Alonso ya samu babban yabo a shekarun baya saboda irin tsarin wasan da yake amfani da shi, ƙwarewarsa wajen sarrafa matasan ‘yan wasa, da kuma yadda yake gina ƙungiya mai tsari da kuzari.
Rahotanni sun kuma nuna cewa Alonso yana son cikakken tasiri a harkokin ƙungiyar, musamman wajen sayen ‘yan wasa, tsarin wasa, da kuma yadda za a tafiyar da aikin gina ƙungiyar.
