Ƙungiyar yaƙi da cutar daji ta yi jimamin rasuwar jarumi Alexx Ekubo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Yaƙi da Cutar Daji ta Ƙasa NCS, ta shiga sahun miliyoyin ‘yan Nijeriya wajen yin jimamin rashin shahararren jarumin masana’antar Nollywood, Alexx Ekubo, wanda ya rasu a ranar 12 ga watan Mayu, 2026 bayan shafe shekaru 40 a duniya.

Hakan ya biyo bayan fama da jinyar cutar daji ta ƙoda da jarumin ya yi, wanda iyalansa suka sanar da rasuwarsa ta kafar X.

Akan haka ne NCS ta sanar da miƙa ta’aziyyarta ga iyalai, abokai da abokan aikinsa a masana’antar bisa babban rashin jarumin.

Baya ga nasarorin da ya samu a masana’antar, Ekubo sananne ne wajen amfani da kafafen sada zumunta don tallafa wa al’umma da kuma inganta matasa.

Haka kuma, ya shahara wajen wayar da kan jama’a akan cutar daji, wanda da shi aka yi ta yin yawon wayar da kai akan cutar acikin dubunnan ‘yan Nijeriya. An ruwaito cewa ya bayar da gagarumar gudunmawa a tafiyar har na tsawon shekaru bakwai.

Kazalika, NCS ta kuma kirayi al’ummar Nijeriya, ƙungiyoyin ci-gaban al’umma, masu taimakon jama’a da cibiyoyin gwamnati da su taimaka wajen kawo ƙarshen cutar ta hanyar wayar da kai, shirye-shirye da kuma bincike akan ababen da ke haifar da ita tare da taimakawa ta wasu hanyoyin da suka dace.

By Babaji