Kwamandan ISIS da aka halaka na da alaƙa da sace ɗaliban makarantar Dapchi – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hedikwatar Tsaro DHQ, ta sanar da cewa kwamandan ISIS da sojojin Amurka da Nijeriya suka halaka a kwanan nan, wato Abu Bilal Al-Manuki, na da hannu a garkuwa da ɗalibai mata na makarantar Dapchi a Jihar Yobe.

Daraktan yaɗa labaran hedikwatar, Manjo-Janar Samaila Uba ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja.

A cewarsa, atisayen da ya yi ajalin Al-Minuki ya gudana ne ta hanyar rarraba bayanan sirri da haɗin-gwiwa tsakanin dakarun tsaron Nijeriya da na Amurka.

Ya bayyana marigayin ɗan ta’addan a matsayin babban jigo a harkokin ISIS kuma ɗaya daga cikin kwamandodin da suka fi yi wa tafiyarsu hidima.

Uba ya ce, atisayen ya alamta samun babban nasara a yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, yankin Tafkin Chadi da kuma shiyyar Sahel da dakarun tsaro ke yi.

Ana ɗaukar marigayin jigon a matsayin ɗan ta’adda mafi aiki a duniya, wanda ya ƙware wajen shirya ƙaddamar da hare-hare da bayar da umarnin garkuwa da mutane.

Al-Manuki na ɗaya daga cikin mayaƙan ISIS da ke aiki tsakanin ƙasa-da-ƙasa a fannin yaɗa labarai da samar da kuɗaɗe da kuma ci-gaba a harkokin samar da makamai, ababen fashewa da tankunan yaƙi, kamar yadda kakakin sojojin ya bayyana.

Kazalika, Uba ya ce Al-Minuki shi ne wanda ya shirya jigilar mayaƙa zuwa Libiya tsakanin shekarun 2015 da 2016, yana mai cewa gabanin haka, shi ɗin sanannen mamban Boko Haram ne.

By Babaji