Cibiyoyin kwalejin kiwon lafiya tara cikin 31 suka cancanci karantarwa a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya kafa kwamitin da zai tantance kwalejin kimiyya da fasaha da cibiyoyin koyar da kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar.

Shugaban kwamitin Dr Faisal Umar kaita da yake gabatar da rahoton sa ya bayyana wa Gwamna cewa akwai nakasu a tsakanin mafi yawan cibiyoyi masu zaman kansu .
Ya sanar da cewa tara ne kawai daga cikin kwalejoji 31 masu zaman kansu da aka tantance suka cika ƙa’idojin gudanar da aiki.

“Yawancin cibiyoyin da aka ziyarta basu sa ƙwararrun ma’aikata ga kuma ƙarancin kayan aiki” inji Dr Faisal.

À jawabin sa bayan da ya karɓi rahoton gwamna Raɗɗa ya yaba da ƙwazo tare da ƙwarewa da kwamitin ya nuna wajan gudanar da aikin sa.

“Dole ne mu tabbatar da cewa ƙwararrun cibiyoyi ne kaɗai za su iya gudanar da ayyukan su a jihar “inji Dikko.

Gwamnan ya bada umurnin kafa kwamitin da zai bada shawarar aiwatar ta shawarwarin kwamitin.

By ukarofi