Majalisar Wakilai ta amince da sabuwar dokar haraji ta Tinubu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Majalisar wakilai ta Nijeriya ta amince da ƙudurorin gyaran haraji guda huɗu da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, bayan nazarin rahoton da kwamitin musamman ya yi a ranar Alhamis, 13 ga Maris, 2025.

Daga cikin ƙudurorin akwai ƙudurin dokar da ke tanadin kimanta, tattara, da lissafin kuɗaɗen da ke shiga asusun tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, tare da fayyace ikon hukumomin haraji da sauran abubuwan da suka shafi batun. Haka zalika, an amince da dokar da ta soke dokar kafa hukumar kuɗin shiga ta tarayya (FIRS) ta 2007, tare da samar da sabon ƙudurin da zai kafa hukumar kuɗin shiga ta Najeriya (NRS), wadda za ta duba haraji da sauran kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Sauran ƙudurorin sun haɗa da kafa hukumar haɗin gwiwa kan haraji, kotun ƙarar haraji, da kuma ofishin mai kula da ƙorafe-ƙorafen haraji don tabbatar da daidaitawa, tsarawa, da warware taƙaddama da suka taso daga sha’anin haraji a Najeriya. Bugu da ƙari, an amince da ƙudurin da zai soke wasu dokoki kan haraji, tare da samar da kundin dokar haraji don daidaita tsarin haraji na kuɗin shiga, mu’amaloli da kuma kadarori.

By ukarofi