Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Jihar Nasarawa, ta bayyana shirye-shiryen bikin cika shekaru 50 da kafuwar ƙungiyar.
Shugaban riƙo na CAN a jihar, Rev. Dr. Kefas Abari, ne ya bayyana hakan a wata hira da Manhaja ta yi da shi a Lafia, inda ya jaddada cewa bikin shekaru 50 na ƙasa baki ɗaya ne, ba na jihar Nasarawa ba.
A cewarsa, an kafa CAN ne a shekarar 1976 a matakin ƙasa, yayin da Jihar Nasarawa ta yi bikin cika shekaru 30 da kafuwa a makon da ya gabata, don haka bikin na shekaru 50 na ƙasa ne.
Yace an yanke shawarar barin jihohi su gudanar da nasu bikin ne a wani taron majalisar zartarwa ta ƙasa, inda aka amince cewa baya ga bikin na ƙasa, jihohi da ƙananan hukumomi su ma su gudanar da nasu domin a ji tasirin bikin a matakin ƙasa.
“Idan muna maganar ƙungiyar, muna maganar zumunci ne, muna maganar haɗa kowa, ya kamata a tafiyar da kowa tare,” in ji Abari.
Ya bayyana cewa bikin na ƙasa ya fara ne a ranar 2 ga Oktoba kuma zai ƙare a ranar 18 ga Oktoba, yayin da reshen Jihar Nasarawa, bayan la’akari da wasu dalilai, ya sanya nasa bikin a ranakun 10 da 11 ga Oktoba.
Da yake bayyana jerin ayyukan bikin, shugaban CAN ya ce za a gudanar da gangamin wayar da kai a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba da Juma’a, 9 ga Oktoba, inda matasan ƙungiyar za su zagaya cikin birnin Lafia da takardu da fastoci domin wayar da kan jama’a.
Yace a ranar Asabar, 10 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 7:00 na safe, za a gudanar da addu’a ta musamman domin Jihar Nasarawa da Najeriya baki ɗaya a wurin shiga birnin Lafia wato Welcome to Lafia City Gate, wadda za a ɗauki tsawon awa ɗaya.
Abari ya bayyana cewa bayan addu’ar, shugabannin coci-coci da jama’a za su yi tattaki zuwa mahaɗar filin wasa (Stadium Junction) inda za su haɗu da ɗimbin jama’a domin yin gangami zuwa Cocin St. William Catholic Church da ke Lafia, inda zai yi jawabi ga manema labarai.
Ya ƙara da cewa da misalin ƙarfe 3:00 na rana a wannan ranar, ƙungiyar za ta gudanar da taron ƙoli na musamman da kuma bikin bayar da lambobin yabo a cocin ERCC Graceland da ke Lafia.
A cewarsa, za a bai wa wasu fitattun Kiristoci lambobin yabon, ciki har da tsofaffin shugabannin ƙungiyar, ‘yan siyasa Kiristoci da kuma ɗaiɗaikun mutanen da suka sadaukar da kai wajen ci gaban kiristanci a jihar.
“Kowa yana da muhimmanci, kowa, saboda akwai waɗanda suka sa muka zama abin da muke a yau ba tare da mun san su ba, waɗanda suke yi mana addu’a, waɗanda suke yi mana fatan alheri. Amma ba za mu iya bai wa kowa lambar yabo ba. Mun yanke shawarar zaɓen wasu kaɗan,” in ji shi.
Ya bayyana cewa taron ƙolin zai bayyana tarihin CAN, nasarorin da ta samu a cikin shekaru 50 da suka gabata da kuma hanyar da za a bi a gaba.
Abari ya ƙara bayyana cewa a ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, za a gudanar da hidimar godiya ta musamman tsakanin mabiya ɗariƙa daban-daban a cocin ECWA Good News da ke GRA, Lafia, wadda zai haɗa da yabon Ubangiji, addu’o’i, godiya da wa’azi.
Yace da ace akwai dama da reshen ƙungiyar ya haɗa da shirye-shirye na matasa, mata da sauran ƙungiyoyi, amma saboda karancin kuɗi da lokaci.
Da yake magana kan saƙon sa ga al’ummar Jihar Nasarawa, musamman Kiristoci, Shugaban riko na CAN ya ce taken CAN shi ne “Domin su kasance ɗaya”, inda ya jaddada cewa ƙungiyar ta ci gaba da yin addu’ar haɗin kai, zaman lafiya, fahimtar juna, ci gaba da cigaban ƙasa da kuma jikin kiristi duk da ƙalubalen da ta fuskanta a cikin shekaru 50 da suka gabata.
Ya yi kira ga kiristocin jihar da su guji nuna son kai da kuma abubuwan da ke kawo rarrabuwar kai, tare da haɗa kai domin ci gaban coci da jihar.
Abari ya kuma yi kira ga coci da ta cigaba da yin addu’ar samun zaɓe na gaskiya, adalci da sahihanci gabanin babban zaɓen 2027, yana mai cewa CAN ba ta nuna goyon baya ga wani ɓangare ba, sai dai tana tsayawa ne a ɓangaren adalci da gaskiya.
“Addu’armu ita ce Allah Ya kawo mana dan takarar da yake bayan zuciyarsa, wanda yake tsoron Allah, wanda zai zo ya yi wa Allah hidima da kuma yi wa bil’adama hidima, wanda zai zo ya haɗa kowa a Nasarawa a matsayin jiki daya, ba tare da la’akari da ƙabila ko bambancin yanki ba,” in ji shi.
