Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta buƙaci Sufeto-Janar na ’yan sandan Najeriya (IGP), Rilwan Disu, da ya gudanar da cikakken bincike kan zargin neman ko karɓar N700,000 da ake yi wa mataimakin sufeto-janar na ’yan sanda (AIG), Emmanuel Egune.
NBA ta ce idan ba a gudanar da bincike mai zaman kansa tare da ɗaukar matakin da ya dace ba, za ta garzaya kotu domin neman adalci.
Shugaban NBA reshen Gombe, Alhassan Muazu, ya bayyana matsayar ƙungiyar bayan taron wata-wata na reshen, inda ya ce ƙungiyar ta tattara wasu bayanai da shaidu da suka danganci zargin.
Ya ce lamarin ya samo asali ne daga binciken da FCID Annex da ke Gombe ke yi kan Ahmadu Shuaibu Gara, wanda ake zargi da aikata laifin cin zarafi ta kafafen sada zumunta.
A cewar Muazu, an buƙaci Gara ya biya N700,000 kafin a sake shi bisa beli, inda ya ce an biya kuɗin ta hannun lauyan wanda ake zargin, E.S. Tizhe.
Ya ce bayan lauyan ya shigar da ƙorafi kan abin da ya faru, an gayyace shi zuwa FCID Annex, inda daga baya aka yi masa barazanar kama shi.
Shugaban NBA ya ce ƙungiyar ba za ta yi shiru ba kan abin da ta bayyana a matsayin zargin cin zarafi da karɓar kuɗi daga masu neman beli.
“Idan ba a ɗauki mataki ba, za mu kai ƙara ba kawai kan AIG FCID Annex ba, har ma da rundunar ’yan sanda baki ɗaya, ciki har da Police Service Commission,” in ji Muazu.
Ya kuma nuna damuwa kan abin da ya ce jami’an ’yan sanda sun karɓi takardar kiran Tizhe zuwa Bar da katin shaidarsa a lokacin da ake gudanar da belin Gara.
Sai dai AIG Egune ya musanta zargin, inda a wata wasiƙa da ya aika wa IGP ranar 2 ga Oktoba, 2026, ya bayyana cewa binciken ya samo asali ne daga umarnin kotun majistare kan ƙorafin cin zarafin yanar gizo da Alhaji Tanko Isiaka Gwamna ya shigar kan Gara.
Egune ya ce an gayyaci mai ƙorafin da wanda ake zargi, sannan aka karɓi bayanansu, yana mai cewa Gara ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Ya bayyana cewa daga baya Tizhe ya nemi belin gudanarwa, tare da gabatar da jami’in ’yan sanda, Usman Adamu, a matsayin wanda zai tsaya wa Gara.
A cewar AIG ɗin, ya buƙaci lauyan ya gabatar da takardar kiran sa zuwa Bar da katin shaidarsa domin tabbatar da sahihancinsa da kuma samun damar gano wanda aka saki idan buƙatar hakan ta taso.
Egune ya musanta cewa shi ko ofishinsa sun nemi ko karɓi kuɗi daga Gara ko lauyansa, yana mai cewa takardun an miƙa su ne bisa son rai.
Ya ƙara da cewa jami’an binciken sun yi ƙoƙarin tuntuɓar wanda ya tsaya wa Gara bayan an sake shi, amma ba su samu nasarar yin magana da shi ba.
AIG ɗin ya kuma yi zargin cewa a baya an taɓa samun wasu ƙorafe-ƙorafe da suka shafi Tizhe da Gara, ciki har da wani lamari da ya faru a shekarar 2025.
Yayin da NBA ke buƙatar bincike mai zaman kansa kan zargin, FCID Annex ta musanta karɓar kuɗi, lamarin da ya haifar da barazanar ɗaukar matakin shari’a idan ba a warware takaddamar ta hanyar bincike ba.
