Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Babba mai taimakama Gwamna akan shirin cigaban al’umma (CDP) mai kula da ƙananan hukumomi,Rimi, Charanchi,da Ɓatagarawa kuma ,Hon Nu’umanu Muhammad Imma Rimi ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa, inda murabus ɗin ya fara aiki nan take.
Ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aike wa sakataren gwamnatin Jihar Katsina.
A wasiƙar, Nu’umanu wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Rimi ya yi godiya ga Gwamna Dikko Raɗɗa bisa damar da ya bashi ya kawo cigaba a mazaɓar sa.
Ita ma Fadila Sani Dalhatu mataimakiya na musamman kan aiwatar da ayyuka ta yi murabus.
Ya zuwa yanzu masu riƙe da muƙamin siyasa a gwamnatin Dikko Raɗɗa su 8 ne sukai murabus ɗaya bayan ɗaya.
Har ya zuwa yanzu babu wanda ya bayana dalilin ajiye muƙamin sa.
Tuni Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗe naɗen muƙamai bakwai na maye gurabun su.
