
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Kwamandan Sojojin Nijeriya na Shiyya ta 2, Manjo-Janar Auwalu Mahmuda ya bayyana cewa rundunar ta karɓe iko tare da mayar da filin shaƙatawa na Old Oyo National Park cibiyar bayar da horo bayan garkuwa da ceto ɗalibai 40 da malamansu a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
Mahmuda ya faɗi haka ne a ranar Laraba yayin karɓar baƙuncin wakilan ƙungiyar ‘yan jarida ta Chapel of the Nigerian Union of Journalist reshen Jihar Oyo, a hedikwatar shiyyar da ke yankin Odogbo a Ƙaramar Hukumar Akinyele ta jihar.
Ya ce, Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Laftanal Janar Waidi Shaibu ne ya umarci shiyyar tasu ta yi amfani da filin a matsayin wajen bayarwa da karɓar horo ga jami’an sojoji, yana mai cewa tuni sojojin suka aiwatar da umarnin. A cewar kwamandan, an ɗauki wannan mataki ne da nufin hana ‘yan ta’adda amfani da yankin gandun dajin a matsayin maɓoyarsu yayin aikata miyagun laifuka.
“Wannan umarni ya zo ne bayan ceto mutanen Oriire da aka sace. Karɓar da aka yi wa filin a yanzu ya katange masu garkuwa da wasu masu aikata miyagun laifuka da ke amfani da babban yankin dajin a matsayin sansanin miyagun ayyukansu”, inji Mahukunta.
A ranar Juma’a, 15 ga Mayu, 2026 ne ‘yan bindiga suak yi awon-gaba da ɗalibai 40 da malamansu yayin wani farmaki da suka ƙaddamar a makarantu uku da ke yankunan Yawota da Ahoro-Esienle a Ƙaramar Hukumar Oriire. Daga bisani a ranar Juma’a, 10 ga Yuli, 2026 wata haɗakar jami’an tsaro ta yi nasarar ceto su bayan shafe kwana 56 a hannun ‘yan bindigar
Jagoran sojojin ya kuma buƙaci a samar da haɗin-gwiwa mai ƙarfi a tsakanin sojoji da kafafen yaɗa labarai domin magance ayyukan yaɗa labarai masu ruɗarwa da na bogi, yana mai kira ga ‘yan jarida da su riƙa tantance labarai daga sojoji gabanin wallafawa domin kauce wa fuskantar babban ƙalubale.
