Kwana biyu bayan hatsarin jirgin Ondo, wani jirgin NAF ya karci ƙasa a Benuwai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani jirgi mai tashin angulu na Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ya karci ƙasa a Jihar Benuwai a yayin sauka a ranar Laraba a lokacin da yake ƙoƙarin kai wa sojoji agaji a lokacin da suke ƙaddamar da wani atisayen fatattakar ‘yan bindiga, kamar yadda wata majiya ta shaida wa manema labarai.

Da take tabbatar da aukuwar lamarin ta sahihin shafinta, NAF ta bayyana al’amarin a matsayin “saukar kiyayewa”, inda ta ce matuƙin ya yi amfani da ƙwarewarsa ta aiki ne wajen sauka daga nisan mil 10 a sararin samaniya bayan nasarar kammala atisayen.

Saidai, majiyar ta shaida wa ‘yan jarida cewa jirgin ya taɓa ƙasa ne a wata gona da ke yankin Utur Tse-Igboji a Makurɗi, yayin da NAF ta ce jirgin yana daga cikin waɗanda suka taimaka wa atisayen dakaru da ya hari masu garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Ogbadigbo, kusa da iyakar Enugu da Benuwai.

Daraktan Hulɗa da jama’ar NAF, Ehimen Ejodame ya bayyana cewa atisayen ya lalata ayyukan ‘yan ta’adda da taimaka wa dakarun tsaro wajen kutsawa yayin fatattakar masu laifi, wanda hakan ya bai wa dakarun nasara.

Wannan al’amari ya faru ne kwana biyu da jirgin NAF ya yi hatsari a yankin Igbokoda na Ƙaramar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo, wanda ya rutsa da fasinjoji 25 da jami’an jirgi bakwai. Akan haka ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana makokin kwana uku domin karrama jami’an da suka rasu sakamakon aukuwar iftila’in.

By Babaji

Leave a Reply