Emily St. John Mandel: Marubuciyar da ta mayar da ƙarshen duniya labarin rayuwar ɗan Adam

Spread the love

‘Station Eleven’: Littafin marubuciya Emily da ya zama allon kallo bayan annobar Korona 

Daga AISHA ASAS

Masu karatu, barkanmu da sake kasancewa a shafin Adabi na jaridar Blueprint Manhaja, shafin da muke buɗe ƙofofin duniyar marubuta, mu leƙa cikin rayuwarsu, mu fahimci abin da ya motsa alƙalaminsu da kuma dalilin da ya sa wasu labarai suke iya barin soyayya a zuciyar mai karatu. A yau za mu shiga duniyar wata marubuciya wadda ta yi suna wajen rubuta labaran da ke sa mutum ya kalli rayuwar yau da kullum da wata sabuwar fahimta; marubuciya ce da ta iya ɗaukar abin da mutane suka saba gani a matsayin ƙarshen komai, ta mayar da shi farkon tambayoyi game da rayuwa, soyayya, buri da abin da ya rage wa ɗan Adam idan duniya ta sauya.

Sunanta Emily St. John Mandel. Wasu sun san ta ne saboda littafinta na Station Eleven, wanda ya yi fice wajen zana hoton duniya bayan wata annoba ta kawo cikas ga rayuwar bil’adama. Wasu kuma sun san ta ta hanyar The Glass Hotel da Sea of Tranƙuility, littattafan da suka nuna yadda take iya haɗa rayuwar mutane daban-daban cikin labari guda mai zurfi. Amma kafin waɗannan littattafai su kai ta ga masu karatu a sassa daban-daban na duniya, akwai wata yarinya da ta taso a British Columbia, wadda hanyar karatunta ta bambanta da ta sauran yara, sanadin burin zama ’yar rawa da take da, kuma ta samu damar cika wannan burin nata, saidai daga baya ta gano cewa abin da zuciyarta ta fi komawa gare shi shi ne rubutu.

An haifi Emily St. John Mandel a shekarar 1979 a Merville, British Columbia, Kanada. Lokacin da take da shekara goma, iyalinta suka koma Denman Island, wani ƙaramin tsibiri da ke British Columbia, inda ta taso cikin yanayin rayuwa mai nisa da hayaniyar manyan birane. A nan ne wani muhimmin ɓangare na rayuwarta ya samu siffa: ba ta bi tsarin makarantar gargajiya ba, domin iyayenta sun yi mata karatun gida har zuwa lokacin da take da shekara 15. Daga baya ta yi semesters biyu a kwalejin al’umma, amma ba ta samu takardar kammala sakandare ta gargajiya ba.

Wannan ba yana nufin ilimi bai da muhimmanci a gare ta ba, sai dai hanyar da ta bi wajen neman ilimi da gano abin da take so ta bambanta da hanyar da aka saba gani. Tun tana ƙarama ta fara rubutu, amma a lokacin ba ta san cewa rubutu zai zama sana’ar da za ta dogara da ita ba. A maimakon haka, sha’awarta ta karkata zuwa rawa, inda ta samu horo a School of Toronto Dance Theatre, ta yi ƙoƙarin gina makomarta a wannan fanni, har ma ta yi aiki na ɗan lokaci a matsayin ’yar rawa tare da masu shirya rawa masu zaman kansu.

Sai dai yayin da shekarunta suka ƙaru, ta fara ganin cewa rawa ba ita ce hanyar da take son ci gaba da bi ba. A farkon shekarunta na 20, ta fara komawa ga rubutu, tana haɗa shi da ayyukan da take yi domin samun abin rayuwa. Ta yi ayyuka daban-daban yayin da take rubuta littafinta na farko, Last Night in Montreal, wanda aka wallafa a shekarar 2009. Haka ne rubutun da ta fara a matsayin abin da take jin daɗinsa ya rikiɗe zuwa sana’ar da za ta gina rayuwarta a kai.

Abin da ya sa wannan ɓangare na rayuwarta ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda hanyar da ta bi ba ta kasance madaidaiciyar hanyar da aka saba gani ba. Ma’ana ba ta kasance ɗaliba daga makarantar adabi ba, ba ta fara ne da sananniyar mujalla ko wani babban gida na wallafa littattafai ba. Ta fara ne da rubutu saboda tana son rubutu, ta gwada rawa, ta yi ayyukan da ba su da alaƙa da adabi, sannan a hankali ta gano cewa alƙalamin da ta fara riƙewa tun tana yarinya shi ne zai kai ta inda ba ta taɓa tunanin za ta je ba.

Kafin littafin da ya ja duniya zuwa ga tarkon soyayya wato ‘Station Eleven’, Mandel ta riga ta wallafa ‘Last Night in Montreal’, ‘The Singer’s Gun’ da ‘The Lola ƙuartet’. Waɗannan littattafan sun nuna sha’awarta ga labaran laifi, asiri, ɓoyayyun abubuwan da suka faru a baya da kuma yadda zaɓin da mutum ya yi zai iya bin sa har bayan shekaru.

Sai a shekarar 2014 ta wallafa ‘Station Eleven’, littafin da ya zama babban sauyi a rayuwarta ta marubuciya. Littafin ya zana hoton duniya bayan wata annoba ta hallaka mafi yawan al’ummar duniya, amma Mandel ba ta mayar da hankali kan mutuwa da fitintunu kawai ba. Ta shiga cikin rayuwar waɗanda suka tsira, ta tambayi abin da zai sa mutum ya ci gaba da rayuwa idan yawancin abubuwan da ya saba da su sun gushe.

A cikin wannan duniyar da alƙalaminta ya ƙirƙira akwai wata ƙungiyar masu wasan kwaikwayo da mawaƙa da ke tafiya daga wuri zuwa wuri domin gabatar da wasan kwaikwayo. Wannan ƙungiya ta zama wata hanya da marubuciyar ta nuna cewa ko bayan bala’i ya sauya komai, har a irin lokacin mutane na buƙatar fasaha, kiɗa, soyayya da kusanci da juna. Abin da ya sa littafin ya yi tasiri ba wai hoton ƙarshen duniya ba ne, sai dai yadda ya nuna cewa ko a lokacin da komai ya rushe, ɗan adam na ci gaba da neman abin da zai ba rayuwarsa ma’ana.

‘Station Eleven’ ya kasance ɗan takarar National Book Award da PEN/Faulkner Award, sannan ya lashe Arthur C. Clarke Award a shekarar 2015. Daga baya aka mayar da shi jerin shirye-shiryen talabijin. An fassara littafin zuwa harsuna 37, kuma ya sayar da sama da kwafi miliyan 1.5.

A lokacin da Mandel ta rubuta littafin, annobar da ta zana ba wani abu ne da duniya ta fuskanta a irin wannan yanayin ba. Amma bayan bullar Korona a shekarar 2020, masu karatu da dama suka sake komawa ga ‘Station Eleven’, saboda wasu daga cikin abubuwan da littafin ya zana suka fara tunasar da mutane halin da suke ciki. Wannan ya sa littafin ya ƙara samun wata ma’ana a idon masu karatu, ko da yake ba a rubuta shi a matsayin hasashen wata annoba ta gaba ba.

Abin da ya fi jan hankali shi ne, Mandel ba ta yi amfani da ƙarshen duniya domin tsoratar da mai karatu kawai ba. Ta yi amfani da shi ne domin tambayar abin da ya rage wa mutum idan abubuwan da ya dogara da su sun gushe. Idan gine-gine, kuɗi, hanyoyin sadarwa da tsarin rayuwar da muka saba da shi suka ɓace, me zai sa mu ci gaba da rayuwa? Shin mutum zai iya sake samun farin ciki bayan ya rasa abubuwa masu yawa? Kuma shin fasaha tana da wani amfani idan duniya tana cikin bala’i?

Waɗannan tambayoyi ne suka sa ‘Station Eleven’ ya wuce labarin annoba kawai. Ya zama labarin yadda ɗan adam ke neman mafita a cikin duniyar da ta rasa tabbas.

Bayan nasarar ‘Station Eleven’, Mandel ta ci gaba da rubuta littattafan da suka nuna cewa ba ta dogara da labarin annoba wajen jan hankalin masu karatu ba. A shekarar 2020 ta wallafa ‘The Glass Hotel’, littafin da ya haɗa labarin kuɗi, yaudara, ɓacewar mutane da kuma yadda zaɓin mutum zai iya shafar rayuwar wasu. Littafin ya kasance ɗan takarar Scotiabank Giller Prize.

Sai a shekarar 2022 ta wallafa ‘Sea of Tranƙuility’, littafin da ya ɗauki masu karatu zuwa lokuta daban-daban, daga farkon ƙarni na 20 zuwa wasu shekaru masu nisa a nan gaba. A cikinsa ta haɗa batutuwan lokaci, gaskiya, annoba da rayuwar da za ta iya kasancewa da mutum yayin da ɗauki wata hanya dabam.

A nan ne wani tunani da ya daɗe yana jan hankalin Mandel ya ƙara fitowa fili: counter-life, wato rayuwar da mutum bai rayu ba. Me zai faru da mutumin da ya samu kansa a aikin da bai taɓa yi ba? Da ya shiga rayuwar aure? Da ya zauna a sabon gari? Da ya kawar da kai daga sabuwar dama da ta zo ma shi ko ya karɓi damar?

A gare ta, irin waɗannan zaɓuka ba ƙananan abubuwa ba ne. Suna iya sauya mutanen da mutum zai haɗu da su, abubuwan da zai fuskanta da kuma irin mutumin da zai zama. Amma ba wai tana nadamar rayuwar da take ciki ba ne; abin da take bincika shi ne yadda zaɓi guda zai iya buɗe wata ƙofa, yayin da wata ƙofar ta kasance a rufe har abada.

Wannan tunani ya sa rubutunta ya zama kamar madubi da mai karatu zai iya kallon rayuwarsa ta cikinsa. Sau nawa mutum yake tunanin yadda rayuwarsa za ta kasance da ya yi wani zaɓi dabam? Wataƙila da ya ci gaba da wani aiki, da ya zauna a garinsu, da ya karɓi wata dama ko kuma da bai bar wani abokin rayuwarsa ba. Amma rayuwa ba ta ba mu damar komawa baya mu gwada dukkan hanyoyin ba. Abin da muke da shi shi ne rayuwar da muka zaɓa, da kuma damar da muke da ita ta yin wasu sababbin zaɓuka.

Mandel tana ɗaukar wannan tunani ta kai shi duniyar labari, inda mai karatu zai iya ganin yadda mutum zai kasance a cikin yanayi biyu mabambanta. A irin waɗannan labarai, tambayar ba wai wace rayuwa ce ta fi kyau ba ce, sai dai yadda yanayi, mutane da zaɓuka suke gina halin mutum.

Rayuwar Mandel ita ma ta samu sauye-sauye kamar waɗanda take rubutawa. Ta yi aure da marubuci Keɓin Mandel, wanda daga baya suka rabu a shekarar 2022. Tana da ’ya mace, kuma a shekarar 2025 ta sake yin aure da mai ɗaukar hoto Laura Barisonzi. An gudanar da bikin aurensu a Greenlight Bookstore da ke Brooklyn, kuma ’yarta ta kasance tare da ita a lokacin bikin.

Akwai wani abu mai ban sha’awa a wannan ɓangaren na rayuwarta: wurin da aka yi bikin aurenta ba kawai wani wuri ne na biki ba. Greenlight Bookstore yana da alaƙa da duniyar adabin da ta gina kanta a cikinta, abin da kenan ya sa bikin ya haɗu da wani ɓangare na rayuwar da ta shafe shekaru tana ginawa.

A shekarar 2015 kuma ta bar aikinta na yau da kullum domin ta fi mayar da hankali kan rubutu. Wannan mataki ya zo bayan shekaru tana haɗa aikin neman abin dogaro da kai da rubuta littattafai. Barin aiki bai sa ƙalubalen rayuwa suka ƙare ba, amma ya ba ta damar mayar da hankali sosai kan abin da take ginawa a matsayinta ta marubuciya.

Wannan ya sake nuna wani abu game da rayuwarta: nasarar marubuci ba ta fara ne lokacin da duniya ta fara saninsa ba. Akwai shekaru na rubutu ba tare da sanin ko zai yi nasara ba, akwai ayyukan da ba su da alaƙa da abin da mutum yake so, akwai sauye-sauyen rayuwa da kuma zaɓukan da ba za a iya sanin sakamakonsu tun farko ba.

A watan Satumba na shekarar 2026, Mandel ta dawo da sabon littafinta, ‘Eɗit Party’, wanda shi ne littafinta na bakwai. Littafin ya fito ne a ranar 15 ga Satumba, 2026.

A wannan sabon aiki, Mandel ta sake haɗa abubuwan da masu karatu suka saba gani a rubutunta: labarin laifuka, hasashen makomar duniya, halayen da suka fito a wasu littattafanta da kuma tambayar yadda mutum zai ci gaba da rayuwa idan tsarin da ya sani ya rushe.

Labarin ya kai mai karatu zuwa Los Angeles na shekarar 2031, inda Ari Waker ta sake komawa cikin al’umma bayan ta shafe shekaru 18 a gidan yari. Ari ba sabuwar fuska ba ce a duniyar Mandel; ta fito tun a ‘The Singer’s Gun’. Bayan shekaru tana tunanin abin da zai faru da ita, Mandel ta dawo da ita a wannan sabon littafin a lokacin da ta fito daga gidan yari.

Amma lokacin da Ari ta dawo, Amurka ba ita ce wadda ta sani ba. ƙasar ta wargaje bayan yaƙin basasa, wasu yankuna sun balle, California kuma ta zama ƙasa mai cin gashin kanta. Ari da abokiyar zamanta Gloria sun je wata liyafa a Los Angeles, inda abubuwa masu ban mamaki suka fara faruwa: akwai mutane masu kama da waɗanda suke wajen liyafar, sannan mai masaukin liyafar ya ɓace. Daga nan ne labarin ya fara buɗe wata duniya mai cike da tambayoyi game da ainihi, gaskiya da kuma rayuwar da za ta iya kasancewa.

A gefe guda kuma, littafin ya gina wata duniya dabam wadda ba ta cika da hargitsi irin na duniyar Ari ba, sai dai tsarin sa ido da iko mai tsauri. Wannan ya ba Mandel damar sake komawa ga abin da ya daɗe yana jan hankalinta: me zai faru da mutum idan ya shiga wata rayuwa dabam? Shin yanayin da muke ciki ne ke gina mu, ko kuwa akwai wani ɓangare na halinmu da zai kasance iri ɗaya ko da a ina muka tsinci kanmu?

Mandel ta fara rubuta ‘Eɗit Party’ a shekarar 2022. A lokacin ne ta fara gina wannan tunanin na Amurka da ta rabu saboda yaƙin basasa, sannan ta ƙirƙiri wata duniya ta biyu wadda za ta zama tamkar madubin farko: ba hargitsi ba, sai tsauraran matakan iko da sa ido. Ta haka ne littafin ya koma wani bincike kan siyasa, iko, tsoro, ainihi da kuma rayuwar da mutum zai iya samu idan ya kasance a wani yanayi dabam.

Idan aka dubi rayuwar Emily St. John Mandel daga yarinyar da aka yi wa karatun gida a wani ƙaramin tsibiri, zuwa ’yar rawa da ta gano cewa rawa ba ita ce makomarta ba, sannan marubuciyar da littattafanta suka kai ga miliyoyin masu karatu a duniya, za a ga cewa rayuwarta ma tana ɗauke da wasu daga cikin jigogin da take rubutawa.

Ta fuskanci sauye-sauye, ta yi zaɓuka, ta bar wasu hanyoyi, ta buɗe wasu, kuma ta ci gaba da gina rayuwarta a cikin duniyar da ba ta da tabbas. Wataƙila shi ya sa take iya rubuta mutane da ke ƙoƙarin gano kansu a cikin duniyar da abubuwa suka sauya.

A ‘Station Eleven’, ta binciki abin da ya rage wa ɗan Adam bayan annoba. ‘A The Glass Hotel’, ta duba alaƙar mutane da kuɗi, asara da zaɓi. A ‘Sea of Tranƙuility’, ta binciki lokaci, gaskiya da duniyoyin da za su iya kasancewa. Yanzu kuma a ‘Eɗit Party’, ta sake tambayar yadda mutum zai kasance idan duniyar da ya sani ta canza gaba ɗaya.

A ƙarshe, abin da ya haɗa waɗannan ayyuka ba wai annoba, yaƙi, tafiyar lokaci ko duniyoyin gaba kawai ba ne. Abin da ya fi bayyana shi ne mutum da abin da yake nema a lokacin da rayuwa ba ta da tabbas.

By ukarofi

Leave a Reply