Gwamnatin Nasarawa ta ƙara faɗaɗa wayar da kai kan kula da ido – Kwamishina Gaza

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnatin Jihar Nasarawa tace tana ƙara ƙaimi wajen hana cututtukan ido da kuma gano matsalolin ido da wuri a faɗin jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Gaza Gwamna, ta hannun sakataren dindin na ma’aikatar, Dakta Ibrahim Adamu Alhassan, ne ya bayyana hakan a wata hira da Nigerian Tribune a Lafia a ranar Alhamis yayin bikin ranar gani ta duniya wato World Sight Day a turance.

Dakta Gwamna yace ma’aikatar na mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da cututtukan ido, yadda suke faruwa da hanyoyin da za a bi don kare kai daga kamuwa da su.

Yace mataki na farko shi ne horar da ɗimbin ma’aikatan lafiya, musamman a matakin farko, domin su fahimci matsalolin ido, su gano su da wuri kuma su tura marasa lafiya zuwa ga ƙwararru don magani.

“Asibitocin farko sune mafi kusa da jama’a, don haka idan sun gano matsalar ido da wuri, za su iya turawa zuwa asibitocin sakandare da manyan asibitoci domin samun kulawa mai kyau,” in ji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ma’aikatar na wayar da kan malamai, domin sau da yawa matsalolin ido na yara kan ɓace a makarantu.

“Akwai lokacin da ake ganin ɗalibi yana faɗuwa a jarrabawa ba don bashi da basira ba, sai don baya iya karanta abin da ke kan allo ko a littafinsa,” in ji shi.

Yace gwamnati na horar da malamai domin gano yaran da ke da matsalar ido da wuri domin a kai su magani.

Kan magani ga masu matsalar ido, Kwamishinan ya bayyana cewa ma’aikatar ta kafa teburin kula da ido ƙarƙashin jagorancin wani ƙwararren likitan iyali wanda ke tsara yadda za a inganta lafiyar ido.

Yace ma’aikatar na haɗin gwiwa da asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lafia, inda sashen kula da ido ke gano marasa lafiya da yi musu magani ciki har da tiyata da bayar da tabarau.

Ya kuma ce jihar na sa ran wani shiri da zai raba tabarau da yawa ga masu matsalar gani, da magance marasa lafiya da kafa cibiyoyin kula da ido a wasu asibitocin sakandare da na farko.

Kan rawar da abinci ke takawa, Dakta Gwamna ya ce abinci na da matuƙar tasiri ga lafiyar ido, inda ya jaddada muhimmancin bitamin A.

Yace ƙarancin bitamin A na cutar da ido, haka kuma cututtuka kamar kyanda da sanyi na mata (syphilis) na iya haifar da matsalar ido, musamman ga yara.

“Akwai sinadari mai suna bitamin A wanda ke kula da gani. Samuwarsa ko rashinsa yana da matuƙar muhimmanci wajen kula da idanunmu. Idan kana da ƙarancin bitamin A, hakan na shafar idanu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa wasu nakasar ido da ake gani tun daga haihuwa kan kasance ta gado, musamman idan uwa na ɗauke da cutar syphilis, wanda kan haifar da haihuwar yaro da cutar.

Da yake magana kan taken bana na ranar ganin na duniya mai taken “Ku So Idanuwanka”, yace ido taga ce ta duniya kuma dole ne a kare shi daga raunuka da haske mai cutarwa.

Ya shawarci masu sana’o’i kamar masu babura, masu walda, masu aikin katako, masu hakar ma’adinai, manoma da masu yankan ciyawa da su kula da idanunsu sosai.

Ya kuma shawarci jama’a da su ci abinci mai dauke da bitamin A, inda ya ce an riga an gina abinci da yawa da sinadarin kamar sukari, gishiri, dankalin Hausa da masara.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa duba idanunsu akai-akai, inda ya ce masu ƙasa da shekara 40 su riƙa dubawa sau daya a shekara, yayin da masu shekara 40 zuwa sama su riƙa dubawa duk bayan wata uku zuwa shida.

“Sau nawa ya kamata mu riƙa duba ido? Wata ƙila sau ɗaya a shekara ga waɗanda ba su kai shekara 40 ba, amma da zarar ka kai shekara 40, idan kana kusa da shekaruna, to ya kamata ka riƙa dubawa duk bayan wata uku ko shida domin ka kula da idanunka yadda ya dace,” in ji shi.

Haka kuma, wani ƙwararren likitan ido a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lafia, Dakta Akpa E. Noah, ya ce bikin ranar ganin duniya na bana a Jihar Nasarawa ya haɗa da duba marasa lafiyar ido da ba su shawara.

Yace sashen kula da ido na asibitin ya shirya ayyuka da dama don bikin ranar, ciki har da gwajin ido, magani ga wasu marasa lafiya da kuma ba da shawara.

Yace taron na kwana ɗaya ya kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin duba ido akai-akai da kuma hana makanta da za a iya kaucewa.

Yace bikin na da nufin wayar da kan jama’a kan lafiyar ido da kuma tabbatar da cewa masu matsalar ido sun sami kulawa cikin gaggawa.

Ya ƙara da cewa sashen zai ci gaba da haɗin gwiwa da ma’aikatar lafiya ta Jihar Nasarawa da sauran abokan hulɗa domin inganta ayyukan kula da ido a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply