
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi alla-wadai da zargin cin zarafi da wulaƙanta Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan da aka ce wasu ‘yan Nijeriya sun yi a Birnin Landon, Ingila. Ya bayyana al’amarin a matsayin “hari kan alƙalin wasa gabanin take wasan ƙwallon ƙafa”, yana mai gargaɗin irin haka ka iya tauye martabar dimukraɗiyya da yin dameji ga kimar Nijeriya a idon duniya.
Tsohon ɗan majalisar ya bayyana haka ne a wani rubutu da aka wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, inda ya yi ƙalubalen cewa mai ya sa za a farmaki shugaban INEC ɗin kan zaɓen da ba a riga an gudanar ba. Ya bayyana cewa, har yanzu zaɓen 2027 na da sauran lokaci duk da cewa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara sun fara gudanar da harkokin zaɓe kuma suna yawon neman zaɓe a sassan ƙasar.
Akan haka ne ya Shehu Sani ya kamanta zargin harin na kan Amupitan a Landon da farmakin da ‘yan dabar siyasa suke kai wa domin tayar da hargitsi acikin al’umma a Nijeriya. Ya ce, cin zarafin shugaban hukumar zaɓen Nijeriya kan saɓanin siyasa ya ci karo da biyayya ga martabar dimukraɗiyya daga ɓangaren ‘yan ƙasa. “Mene ne bambanci abin da suka yi da waɗanda ɓata-gari ke yi wajen zagi da wulaƙanta wasu a gida?”
Sanatan ya kuma yi gargaɗin cewa bai dace a bari bambance-bambancen ra’ayoyin siyasa suna haifar da kai farmaki, wulaƙanci ko haifar da yamutsi ba acikin tarukan al’umma. Kazalika, ya koka kan yadda hakan ka iya yin tasiri a matakin ƙasa-da-ƙasa musamman ganin yadda bidiyon aukuwar lamarin ya karaɗe kafafen sada zumunta.
A cewarsa, wannan zai sa a riƙa yi wa ‘yan Nijeriya da ke ƙasashen waje mummunan fahimta da haifar da wasu tambayoyi kan salon siyasar ƙasar, yana mai cewa cikakken nuna dattako a siyasa shi ne girmama cibiyoyin dimukraɗiyya da barin jami’an gwamnati su yi aikinsu ba tare da wata tsangwama ba. Har ila yau, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ƙaurace wa dukkan abin zai tayar da zaune-tsaye da miƙa kokensu na siyasa ta halastattun hanyoyi bisa tsarin dimukraɗiyya a matsayin mayar da al’amarin cin zarafi, musamman ganin yadda ake ƙara kusantar zaɓukan 2027.
