
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Masu kishin Arewa ta CNP, ta koka tare da alhinin mutuwar wata ɗalibar Jami’ar Tarayya ta Gusau dake Jihar Zamfara, wadda ta rasa ranta a hannun ƴan bindiga.
Ɗalibar mai suna Zarah Abubakar Shehu mai shekaru 21, an sace ta ne tare da ƴan uwanta a ranar 3 ga watan Nuwamba, 2024.
Bayan shafe watanni huɗu a hannun ƴan bindigar ne, cikin rashin tausayi ta rasa ranta a hannunsu.
A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na CNP, Genshak W Wuseli Golak ya fitar, ƙungiyar ta ce ta yi jimamin rashin matashiyar a sanadiyyar gazawar gwamnati da ƴan ta’adda marasa tausayi.
Da farko, ƴan bindigar sun buƙaci a biya su Naira miliyan 35 ne a matsayin kuɗin fansa, wanda daga bisani suka rage zuwa miliyan N10, inda daga baya kuma suka buƙaci a haɗo masu da babura guda huɗu da kwalin baƙin mai guda huɗu.
Baya ga haka ne sai aka sanar da cewa, Zarah ta rasu kuma sun binne ta kamar dabba cikin rashin mutuntawa har bayan ta mutu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
CNP ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta farauto waɗanda suka aikata mummunan aikin tare da hukunta su.
Ta kuma ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara kan rashin adalci game da tsaron rayukan al’umma musamman marasa galihu, ta na mai cewa lamarin ya wuce a ce an yi alla-wadai, don haka a yi adalci wajen kare dukiyoyi da rayukan al’ummar ƙasa.
