
Daga BELLO A. BABAJI
Da farko, Blueprint ta ruwaito cewa Meranda Mojisola ta yi murabus daga muƙamin, yayin da Mudashiru Obasa ya sake zama Kakakin Majalisar.
A wani jawabi da ta fitar a ranar Litinin, Meranda ta ce ta yi hakan ne don cigaba da kare martabar Majalisar Dokokin.
A ranar 13 ga watan Junairu, 2025 ne Meranda ta zama Kakakin, wanda hakan ya haifar da cecekuce da rikici acikin ƴaƴan majalisar da yin barazana ga haɗin-kan mambobinta.
Ta ce, ta sadaukar da jagorancin ne don kashe wutar shugabancin majalisar da la’akari da maslahar al’umma.
Ta kuma ce, rashin yin murabus daga muƙamin barazana ce ga harkar demokraɗiyya a majalisar, ta na mai cewa burinta shine a samu shugabanci na gari da kuma bada kariya ga mutanen kirki na jihar.
Meranda ta kuma yi godiya ga ƴan majalisar bisa goyon baya da ta samu daga gare su, waɗanda sun taimaka wajen yanke hukuncin nata wanda ta ce hakan zai taimaka wajen cigaba da gina majalisar da ɗora ta akan daidai.
