Cutar korona: Nijeriya ta karɓi tallafin rigakafin AstraZeneca 699,760 daga Birtaniya

A Talatar da ta gabata Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin korona samfurin AstraZeneca-Oxford guda 699,760 ta hannun COVAX a matsayin tallafi daga Ƙasar Birtaniya.

Muƙaddashin jakadan Birtaniya a Nijeriya, Gill Atkinson tare da sauran manyan jami’ai ne suka ya yi tarayya da shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya, Dr Faisal Shuaib, wajen ƙaddamar da rigakafin.

An ƙaddamar da maganin ne a ɗakin sanyi na ajiyar magunguna da ke daura da Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Rigakafin da Nijeriya ta karɓa ɗin wani ɓangare ne na rigakafin AstraZeneca ƙwaya milyan uku da Birtaniya ta tallafa wa wasu ƙasashen Afirka su 11 da shi don agaza musu wajen yaƙi da cutar korona.

Ƙasshen da suka ci gajiyar wannan tallafin sun haɗa da Zambia wadda ta samu rigakafi ƙwaya 119, 200, Tarayyar Kongo ta samu ƙwaya 51,840, Malawi ta samu 119,040, Senegal ta samu guda 140,160, Masar ta samu 299,680, yayin da ƙasar Uganda ta samu rigakafi 299,520 da sauransu.