Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya naɗa kansa shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓensa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC yayin tunkarar babban zaɓen 2027.

Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya fitar da jaddawalin mambobin a wata takarda da ya fitar a yau Asabar.

Kwamitin ya ƙunshi; Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar, Hope Uzodimma a matsayin sakatare sai Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a muƙaman shugaba da mataimaki. Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman sune mataimakan sakatare na ɗaya da ta biyu.

A cewar sanarwar, shugaban kwamitin, Shugaba Tinubu zai yi aiki tare da tawagar masu bayar da shawara da suka haɗa da Chif Bisi Akande, Chif Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha, Sanata Abdullahi Adamu, da kuma Sanata Florence Ita Giwa.

Haka kuma, sanarwar ta ce Shugaba Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe mataimaka Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen a shiyyoyin Kudu da Arewa. Za su aiki ne tare da Sanata Bamidele Opeyemi da Sanata Jibril Barau a yankunan biyu.

Sanata Adams Oshiomhole na Jihar Edo kuwa, shi ne mataimakin darakta janar na tattarawa da haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya, yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila zai yi aiki a matsayin darakta janar na gudanarwa. James Abiodun Faleke, wanda ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen 2022/2023, shi ne mataimakin darakta janar na shirye-shirye, tsare-tsare da sanya ido kan zaɓe.

Faleke zai yi aiki da daraktocin shiyyoyi, da Sanata Olushola Adeyeye a Kudu maso Yamma, Dakta Ngozi Olejeme a Kudu maso Kudu, Sanata Uche Ekwunife a Kudu maso Gabas, Muntaqha Rabe a Arewa maso Yamma, Ahmed Muhammed Ketso a Arewa ta Tsakiya, da kuma Sanata Sani Ɗanladi a Arewa maso Gabas.

Su kuma Mis Stella Okotete, Injiniya Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori sune sakatarorin Cibiyar Shirye-shiryen Zaɓe. Muiz Adeyemi Banire ne zai jagoranci cibiyar shari’a tare da Dakta Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin mataimaka. Sauran mambobin sun haɗa da Frins Lateef Fagbemi, tsohon gwamna Ibrahim Shema, Worgu Boms da kuma Dakta Kingsley Tochukwu Udeh.

Har ila yau, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, zai yi aiki a matsayin daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa tare da Dele Alake, Bayo Onanuga, da Lanre Issa-Onilu. Sannan, acikin tawagar akwai su Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala, da Felix Morka, a matsayin mataimaka daraktocin tsare-tsare.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da aka kaɗa gangar siyasar 2027, inda ‘yan takara a jam’iyyun siyasa daban-daban suka fara yaƙin neman zaɓensu a matakai da dama tun daga kujerar shugaban zuwa kan gwamnoni, ‘yan majalisun dokokin ƙasa da na jihohi.

By Babaji

Leave a Reply