Da Ɗumi-ɗumi: Hukumar Kula da Fetur na shirin ɗauke muhimman sassanta zuwa Legas

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Man Fetur ta Ƙasa da aka fi sani da Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission a Turance, na duba yiwuwar ɗauke wasu muhimman sassanta zuwa Legas, kamar yadda wata takardar bayani wadda News Point Nigeria ta samu leƙawa ta nuna.

Takardar mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2024 ta ce, an yanke shawarar haka ne domin bunƙasa ayyukan hukumar, rage yawan kuɗin da hukumar ke kashewa wajen gudanar da ayyukanta da kuma tabbatar da hukumar na morar kadarorinta a Legas.

A cewar takardar, “Bisa manufar bunƙasa ayyukan hukumar da cigaban masana’anta da kuma tattalin ofishi a Abuja, muna nazarin yiwuwar ɗauke wasu sassa (na hukumar) zuwa Legas.

“An ɗauki wannan mataki ne domin buƙatar bunƙasa harkokinmu da rage yawan kuɗaɗen da muke kashewa wajen ayyukanmu……”, in ji sanarwar.

Wannan na zuwa ne makonni bayan da Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar za ta ɗage wasu muhimman sassan Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Hukumar FAAN zuwa Legas, lamarin da ya haifar da cece-kuce a sassan ƙasa.

By Editor