Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu gungun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutum tara a kan hanyarsu ta dawowa daga bikini maulidi da ya gudana a Abuja kwanan nan.
Rahotanni sun nuna waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin ‘yan asalin garin Ɗangulbi ne da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Yazuwa haɗa wannan rahoton, babu wani cikakken bayani game da batun.
Majiyarmu ta tattaro cewar, har zuwa haɗa wannan labarin ‘yan ta’addan ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka yi garkuwan da su ba.
Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Alhaji Ghazali da Alhaji Hamza, Zakiru Rabiu, Malam Nazir, Zakiru Samaila, Abdussalamu, Tijjani, Rabiu da Kuma Kamilu Ɗangulbi.
A cewar majiyarmu, baki ɗayansu an yi garkuwan da su ne a cikin mota guda bayan kuma sun shiga yankin jiharsu ta Zamfara.
A hannun guda, duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Asp. Yazid Abubakar, hakan ya ci tura.
