Rubutacciyar waƙa ta masu ilimi ce, waƙar baka kuwa ta kowa ce – Malumman Matazu

“Duk wanda yake yin rubutacciyar waƙa zai iya waƙar baka”

Daga AISHA ASAS 

A wannan satin dai ba bako shafin adabi ya kawo wa masu karatu ba, kasancewar mun saba kawo shi a bangarori da dama na adabi. Don haka za mu wuce kai tsaye ga tattaunawar. 

Idan kun shirya Aisha Asas ce tare da Malumman Matazu:

MANHAJA: Duk da ba ka kasance bako a jaridar Manhaja ba, za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?

MALUMMAN MATAZU: Bismillahirrahmanirrahim. Da farko dai cikakken sunana shi ne: Abdulhamid Muh’d Sani Matazu (Malumman Matazu). An haife ni a Gidan marigayi liman Malam Bala Babban limamin Matazu, a cikin garin Matazu Karamar Hukumar Matazu, Jihar Katsina. Na fara karatun allo ga mahaifina tun ina karami, bayan kammala firamare a Matazu, mahaifina liman Malam Sani ya kai ni makarantar allo a garin Bauchi, bayan nai saukar Alkur’ani, na je wasu garuruwan don karin karatun na Alkur’ani, daga baya na dawo Bauchi in da na cigaba da karatun, tare da kuma shiga karatun zamani a makarantar Bauchi Institute for Arabic and Islamic Studies, bayan kammala Grade two sai kuma nai NCE.

Yanzu haka ina dakon sakamakon karshe na digiri da na kammala a Kwalejin ilmi ta tarayya da ke Katsina, Reshen jami’ar Bayero da ke cikin FCEn ta KATSINA.

Ina cikin sha’irai talatin da jami’ar Usmanu Danfodiyo, da ke Sakkwato ta zabi wakokin da sha’irai fiye da dari biyu sukai a kan matsalar tsaro da ta addabi Arewacin Najeriya, sai ta tantance mutum talatin ina cikin talatin din, ta kuma gayyace mu zuwa jami’ar ta karrama mu.

Na wallafa wakoki mabambanta kan al’amurran da suka jibinci ilmantarwa, tarihi, fadakarwa, nishadantarwa da makamantasu.

Kadan daga cikin wakokin akwai: Wakar ‘Gagara gwari’, ‘Tarihinmu’, ‘Lafiya’, ‘Ido da Amfaninsa’, ‘Talakalmi da Amfaninsa’, ‘Danfarkarmi’, ‘Musabbabi’, ‘Matar Farko’, ‘Danyen Hukunci’, ‘Muhimmancin Ribatar Lokaci’, ‘Ilmi’, ‘Ahlul-Baiti (AS)’, ‘Illar Miyagun Kwayoyi’, ‘Illar Sauro’, ‘Malamin Makaranta’, ‘Likita’ da amfaninsa da kuma Alfiya wato baitoci dubu na yabo ga Manzon Allah (SAW).

Dalibai daga jami’o’i da kwaleji-kwaleji malamansu na turo su gare ni don yin aikin binciken wakokin nawa, don cika gurbin cikar karatunsu, daga ciki kuwa har da masu karatun PH’D da mastas.

Masu shirya tarurruka sukan gayyace ni, in rera musu rubutattar waka, a kan maudhu’in da suka bukata don kara armasa musu taronsu. Ana saka wasu wakokina a rediyo don amfanuwar al’umma.

Kasancewar gidanmu gida ne na malamai, kuma ni ma aikina bai wuce koyon karatun ba, da kuma koyarwa, watakila don haka Maigirma Fagacin Katsina Hakimin Matazu Alhaji Iro Maikano ya nada ni sarautar Malumman Matazu, wanda yanzu haka nake rike da sarautar. Ina da matuqar son nazarce-nazarce, tafiye-tafiye sharhi da bincike. Ina da iyali da yara maza da mata ina zaune a garinmu Matazu.

Ka kasance fitaccen marubucin wakokin Hausa, kuma ka kai makura a kan ta, don haka za mu so kai mana cikakken bayani a kan mece ce rubutattar waka, daga yadda masana ke kallonta da kuma ku marubutanta?

Babu shakka masana sun kebe Rubutacciyar Waka, sun bambance ta da wadda ba rubutatta ba, ga misali daga wasu masana kan ma’anarta kamar haka:

1. “Rubutacciyar Waka sako ne da aka gina shi kan tsararriyar ka’ida ta baiti, dango, rerawa kari (bahari), amsa-amo (kafiya), da sauran ka’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zabensu da amfani da su cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba.” (Dangambo 2007:6)

2. Rubutacciyar Waka wata hanya ce ta gabatar da wani sako a cikin kayyadaddun kalmomi da aka zablba, wadanda ake rerawa a kan kari da kafiya a cikin baitoci (Mukhtar. 2005:2).

3. “Rubutacciyar Waka ita ce wadda aka tsara aka rubuta ta a takarda don a karanta.” (B.Sa’id. 2005).

Da yawan marubutan rubutattar waka, ba malaman rubutattar wakar ba ne, da yawansu baiwa ce Allah ya ba su na iya tsara baitukan, da yawansu sai dai kawai su ga suna iya tsara baitukan, don haka wasu daga nan sai su bazama neman ilmin wakar, wasu ma ba ruwansu da neman ilminta, su dai kawai sha’irai ne, in kuma sun tsara waka, duk sanin masani ba zai ce ba su iya ba.

Ni yadda na dauki ma’anar waka a takaice shi ne: “Waka wata hikima ce cikin hikimomin da Allah ya ke ba, bayinsa”.

Wanda Allah bai ba shi wannan hikimar ba, komai son sa da ya tsara baitukan waka, ba zai iya tsarawa ba. Wannan shi na dauka ma’anar waka a takaice.

Kasancewarka wanda yake yin rubutattar waka, shin kana ganin duk mai yin rubutattar waka zai iya yin wakar baka?

Uhmm! Ai duk wanda yake yin rubutattar waka, to yin wakar baka a wurinsa ba wani aiki ba ne.

Ai rubutattar waka aiki ne na masana, domin kuwa duk wanda yake yin rubutattar waka, to wajibi ya iya karatu da rubutu, amma kuwa wakar baka, ko da baka da duka biyun can za ka iya yin ta, in dai har kana da baiwar yin wakar, sabanin rubutattar waka, ita in baka iya rubutawa ba, bata yiwuwa. in dai ba wanda ya iya rubutun za ka nema, kana fada shi kuma yana rubuta maka.

Ni kaina nan akwai wata firamare da na karantar, na kirkiri wakar baka ban san iyaka ba, kuma a duk lokacin da na ga dama nakan iya kirkirarta, amma rubutattar waka wata ran haka za ka zauna da takardarka da bironka, amma haka za ka tashi, in Allah bai kawo ta ba.

Rubutattar waka da wakar baka wacce ka ke ganin an fi zuba dimbin basira a ciki?

Ai wannan amsar a fili take, domin kuwa ita rubutattar waka, bayan dimbin baiwa da mai ita ke da shi, kuma kari yana da ilmi, kuma ka ji dimbin zalaka a fili ai sai rubutattar waka, domin a cikinta a kwai awo, akwai Amsa amo (Kafiya) uwa uba kuma kawo tsofaffin kalmomi da zaben kalmomi masu cike da hikima da wahalar gano ma’ana.

A shekarar 2022 lokacin da kake farko-farkon fara karatunka na digiri a Jami’ar Bayero reshenta da ke cikin Kwalejin Tarayya da ke Katsina, mun ji kwalejin ta karrama ka, da ‘Azancin Daliban FCE Katsina’, duk da cewa ba karatun Hausa ka ke yi a makarantar ba. Ya abin yake ne?

Kamar yadda na baki labari dazu tabbas Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ta saka gasar rubuta rubutattar waka, a kan matsalar da muke ciki ta tsaro, a wannan yankin namu na Arewa. jami’ar ta fahimci cewa, sha’irai akwai rawar da za su iya takawa, don ba mahukuntan kasar nan shawara don magance matsalar ta tsaro. Su masana suna sane da cikakken hangen nesa da Allah ya ba sha’irai, watakila don haka suka ga ya kamata a gayyato mu don ji daga gare mu.

Saboda haka a ranakun Litinin, Talata da Laraba wato 12, 13 zuwa 14 na july 2021 muka fara taron tantance zakarun sha’iran, in da bayan kammalawa aka karrama mu iya karramawa, aka bamu takardun musamman don yabon aikin da mukai, muka kuma ci abincin dare a liyafar musamman da aka shirya mana da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis da dukkan manyan mukarrabansa.

Bayan dawowarmu gida na koma makaranta Katsina, don cigaba da karatun da nake yi a can.

Wata rana ina makarantar sai na ji daliban da ke nazartar Hausa, suna hira tsakankaninsu cewa, gobe za sui taron Hausa, a babban dakin taron makarantar.

Washegari kuwa nai sa’a ban da lakca a daidai lokacin da za a fara taron, hakan yasa nai wanka na dauko takardun da aka ban a sakkwato, ina isa na samu daya daga cikin dalibai masu shirya taron, nai masa bayanin abin da nake son na gabatar na rera ko da dan tsakure ne a cikin wakar da nai kan matsalar tsaron da Jami’ar Danfodiyo ta karrama ni saboda ita.

Dalibin ya ce in je in samu Dakta Mustafa Abubakar Sadiq wato shugaban sashen na Hausa na kwalejin baki daya. akai kuwa sa’a ni ma malamina ne don shi ne ya dauke mu kos din “Survey of Hausa written literature”. Lokacin da naje aro a karatun da nake na: BA(ed) Islamic studies.

Bayan nai masa bayani, Dakta ya amince za a ban minti 4 zuwa 6 don in gabatar da abin da nai kudiri, na ba shi takardar da sauran kayayyakin da na samo a Sakkwato, bayan ya dudduba ya yaba mani ainun, ya kuma tafi ya kai wa babban bako ga taron, da take kan babbar kujera, wato shugaban kwalejin Dr. Aliyu Idris Funtuwa, ba a jima da fara taron ba aka kira ni na rera wakar ta tsaro da na saka wa suna: ‘Kowa ya tuna bara…’ Lokacin da shugaban kwalejin ya ke jawabinsa ya yaba mani ainun, ya kuma ce da na sanar da kwalejin zan je Sakkwato, don wannan taro da ya hada ni da ‘yan rakiya tare da daukar dawainiyarmu na zuwanmu da dawowa. amma duk da haka yai man kyauta ta ban mamaki a ranar wannan taro, ya kuma cewa shugaban sashen su sanya rana ta musamman don karrama ni.

Haka kuwa akai, domin kuwa a Laraba 30 ga Nuwamba 2022 akai taro na musamman don karramawar, in da aka karramani da mukamin ‘Azancin Daliban Hausa’ na kwalejin bakidaya. An ban takarda rubutatta tare da kambi na musamman. Wannan yana cikin manyan nasarorin da na samu a kan aikin adabina.

Ko wadanne nau’in marubuta akwai dalilin fara rubutunsu, kai yaushe ka fara rubutun waka?

Babu shakka na fara rubutun waka ne, tun lokacin da nake makarantar allo a Bauchi, Unguwar Bakin Kura da nake a Baucin, muna makwabtaka da zawiyyar Sheikh Aminu, a wannan zawiyya daga lokaci zuwa lokaci sha’iran da ke zawiyyar suna yin kasidu kan yabon Annabi (SAW) a cikin sha’iran akwai wani kwararre sosai mai suna Alhaji Sani Uba. yana yin wata kasida da tafi yi man dadi a cikin kasidunsa, to sai na dauki irin karinta ni ma na tsara tawa, har ma na rika rerawa wasu cikin abokan karatun nawa, to a cikinsu sai aka samu wasu suna yin makamancin karin suna zolayata.

Da yake akwai yarinta, sai abin ya rika damuna, daga nan sai na washi wakar ma bakidaya.

Ban kara komawa ta kan waka ba, sai da na dawo gida Matazu, shi ma sai a shekarar 2013 bayan rasuwar shugaban makarantar Matazu Intergrated learning academy wadda nake aiki a lokacin, mai suna Malam Musa Musa Dan’azumi, babu shakka lura da gudunmuwar da ya bada, a harkar ilmi a yankinmu na ga ya kamata ai wani abu na karramawa gare shi, don haka sai nai aniya na rubuta masa wakar ta’aziyya.

Wakar ta karade yankin musamman tsakanin ma’abota karantarwa da dalibansu a makarantun firamaren yankin. Karvuwarta ne ma yasa, hukumar ilmin karamar hukumar ta lokacin tai man alkawarin fadada aikin, amma sai ta ki cika alkawarin, rashin cika alkawarin shi ya kara man kwarin gwiwar cigaba da fafutika, hakan ya sa na kara rubuta wasu wakokin a kan ilmi, lokaci, zumunci da kuma firgici, wakar ‘Firgici’ kuwa ita tai man sanadin fara saka wakokina a rediyo.

Waka ce da ke bayani kan halin da Arewa ta shiga a lokacin na tashin bamai-bamai, satar ‘yan mata da sauran matsalolin da Boko-haram ta kawo mana a yankin Arewa.

Zuwa yanzu wacce fa’ida ka ke ganin an samu daga shawarwarin da ku sha’irai ku ka bayar a wakokinku, musamman ma da shugaban jami’ar ya tabbatar wa mahalarta taron naku cewa za su isar da shawarwarin da ku ka bayar a cikin ga mahukunta?

Alhamdulillah! tabbas zuwa yanzu da yawan shawarwarinmu mahukunta sun dauke su, babbar shawarar da kusan duk sha’iran sun bayar da ita a wakokinsu, kuma mun ga mahukunta sun karbe ta ita ce: ta samar da runduna daga mutanen yankunan da ake da matsalar, kuma Katsina ta fara, daga nan Sakkwato tayi, ga shi Zamfara ma ta yi. mu da ke wuraren ma matsalar nan ke da kamari, babu shakka muna ganin alfanun wannan yunkurin na gwamnonin wadannan jihohi.

Babba cikin shawarwarin da muka bayar shi ne gyara halayenmu, tare da tsaya kyam ga addu’o’in samun mafita ga wannan matsala ta tsaro da ta addabi yankin na Arewa, kuma Alhamdulillah al’ummarmu ta kara fadaka ga kara kaimi ga addu’o’in.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.