Da Ɗumi-Ɗumi: Mahaifiyar El-Rufa’i ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya shiga jimami sakamakon rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufa’i yayin da ake tsaka da shari’a akansa.

Hajiya Umma ta rasu ne yau Juma’a da rana, saidai ba a samu cikakken bayanin yadda al’amarin ya faru ba yayin haɗa wannan rahoto.

Jikanta, Bello El-Rufa’i ya sanar da haka ta kafar sada zumunta a wani yanayi na ban tausayi.

Ya ce, a madadin iyalan El-Rufa’i, yana sanar da al’umma rasuwar hajiyar tare da roƙon su da su sanya ta acikin addu’o’insu na fatan samun rahamar Allah a gare ta.

Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacin da El-Rufa’i ke fuskantar tuhume-tuhume da Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ke masa a kotu.

A kwanan nan aka gurfanar da tsohon gwamnan akan tuhumar sa da hannu a laifuka 10 masu alaƙa da sauya akalar kuɗaɗen jiharsa, lamarin da ya sa ya shafe tsawon kusan wata guda a tsare.

Daga bisani kotu ta ɗage sauraron shari’arsa zuwa ranar 31 ga watan Maris.

By Babaji