Daga USMAN KAROFI
Rahotanni daga ƙasashen duniya sun bayyana cewa ƙasar Iran ta fara shirye-shiryen tsaro inda ake zargin ta tattara sama da sojoji miliyan ɗaya domin fuskantar yiwuwar harin ƙasa daga Amurka. Wannan mataki ya biyo bayan ƙarin tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu, inda ake zargin Amurka na nazarin hanyoyin matsa lamba domin tilasta Iran amincewa da wasu sharuɗɗan sulhu.
Majiyoyin cikin gida a Iran sun bayyana cewa matasa da dama na ci gaba da tururuwa domin shiga rundunar kare juyin juya halin ƙasar (IRGC) da kuma ƙungiyar Basij, domin kare ƙasar daga duk wani hari. Sun kuma nuna cewa Iran a shirye take ta mayar da martani mai ƙarfi idan aka kuskura aka kai mata hari, musamman a yankin mashigar ruwan Hormuz mai muhimmanci ga harkokin man fetur na duniya.
A gefe guda, rahotanni sun nuna cewa ma’aikatar tsaron Amurka na duba yiwuwar ƙara yawan sojoji kimanin 10,000 a yankin Gabas ta Tsakiya, duk da cewa ba a bayyana cikakken shirin kai hari kai tsaye ba. Haka kuma, an ce shugaban Amurka ya ɗan jinkirta wasu matakai na soja domin bai wa tattaunawar diflomasiyya dama kafin ɗaukar mataki na gaba.
Masana harkokin tsaro na duniya na ganin cewa duk wani rikici kai tsaye tsakanin Iran da Amurka zai kasance mai tsanani kuma mai ɗaukar lokaci, saboda ƙarfin soji da dabarun yaƙi na kowanne ɓangare. Duk da cewa Amurka na da fifiko a fasahar yaƙi, Iran na da ƙarfin yawan jama’a da kuma dabarun yaƙin ƙasa da ka iya jawo asara mai yawa ga ɓangarorin biyu.
