Daga USMAN KAROFI
Wani rahoto na musamman da jaridar PRNigeria ta wallafa ya bayyana cewa malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Khalifa Sani Abdulkadir, wanda aka sanar da ɓacewarsa a makonnin baya, yana raye kuma yana hannun jami’an tsaro na tarayya a matsayin “kariya ta musamman.”
Rahoton ya nuna cewa ana tsare da shi ne yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu zarge-zarge da suka shafi tsaro.
Majiyoyi daga ɓangaren tsaro sun ce ana gudanar da bincike kan malamin ne tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya da kuma hukumar DSS, bisa zargin alaƙa da wani yunƙurin juyin mulki da aka daƙile. An ce binciken ya ta’allaƙa ne kan wasu kuɗaɗe kimanin naira miliyan biyu da aka gano an tura su zuwa asusun bankinsa daga wani jami’in soja da ake zargi da hannu a lamarin.
Sai dai iyalan Sheikh Khalifa sun musanta duk wani zargi na aikata laifi, inda suka bayyana cewa kuɗin da aka tura masa ba komai ba ne illa sadaka ko kyautar ibada daga wani mabiyi da ya nemi addu’a. Sun ce babu wata tattaunawa ta siyasa ko wani shiri na laifi da ya shafi malamin, kuma abin da ya faru al’ada ce da aka saba gani tsakanin mabiya da malamai a Arewa.
A halin yanzu dai an kai ƙarar batun zuwa kotun tarayya da ke Abuja domin neman a sake shi, inda aka riga aka saurari shari’ar sau biyu, kuma an ɗage zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2026 domin yanke hukunci. Ci gaba da tsare malamin ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiyansa, yayin da hukumomi ke cewa za a ci gaba da riƙe shi har sai an kammala bincike.
