Da Ɗumi-Ɗumi: Soludo na APGA ya lashe zaɓen Anambara karo na biyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Chukwuma Soludo na Jam’iyyar APGA ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambara a karo na biyu biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 21 na jihar da Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi a yau Lahadi.

INEC ta sanar da cewa jimillar masu zaɓe 584,054 ne suka kaɗa ƙuri’a a jihar, inda gwamnan ya samu ƙuri’u 422,664, lamarin da ya ba shi damar doke Nicholas Ukachukwu na jam’iyyar APC da ya samu guda 99,445 a matsayi na biyu.

Sauran ƴan takarar sun haɗa da na ADC mai guda 8,208, sai na PDP da ya samu jimillar ƙuri’u 1,401.

Ga yadda sakamakon ya kasance a ƙananan hukumomin kamar yadda IntelRegion ta ruwaito:

Dunukofia LGA
APC: 3,284 | APGA: 14,892 | LP: 71 | PDP: 16

Awka North LGA
APC: 3,661 | APGA: 15,895 | LP: 299 | PDP: 203

Njikoka LGA
APC: 5,687 | APGA: 22,213 | LP: 311 | PDP: 47

Nnewi South LGA
APC: 9,281 | APGA: 17,286 | LP: 73 | PDP: 12

Nnewi North LGA
APC: 5,441 | APGA: 20,320 | LP: 1,140 | PDP: 45

Ayamelum LGA
APC: 7,478 | APGA: 13,340 | LP: 117 | PDP: 13

Anambra East LGA
APC: 3,108 | APGA: 14,665 | LP: 304 | PDP: 207

Ogbaru LGA
APC: 3,768 | APGA: 22,803 | LP: 347 | PDP: 30

Oyi LGA
APC: 5,118 | APGA: 18,882 | LP: 3,641 | PDP: 16
16

Orumba North LGA
APC: 2,615 | APGA: 24,664 | LP: 131 | PDP: 17

Orumba South LGA
APC: 2,828 | APGA: 19,818 | LP: 16 | PDP: 18

Aguata LGA
APC: 4,125 | APGA: 35,559 | LP: 124 | PDP: 82

Onitsha North LGA
APC: 4,677 | APGA: 24,225 | LP: 500 | PDP: 111

Onitsha South LGA
APC: 4,156 | APGA: 15,742 | LP: 615 | PDP: 73

Anaocha LGA
APC: 5,956 | APGA: 20,118 | LP: 483 | PDP: 42

Awka South LGA
APC: 5,038 | APGA: 27,896 | LP: 520 | PDP: 63

Idemili South LGA
APC: 6,015 | APGA: 17,224 | LP: 276 | PDP: 40

Ekwusigo LGA
APC: 2,973 | APGA: 18,749 | LP: 194 | PDP: 70

Idemili North LGA
APC: 6,383 | APGA: 25,498 | LP: 1,275 | PDP: 125

Ihiala LGA
APC: 4,425 | APGA: 23,557 | LP: 135 | PDP: —

Anambra West LGA
APC: 16,595 | APGA: 71,365 | YPP: 2,871 | ADC: 152

Kimamin ƴan takara 16 ne suka tsaya takarar gwamnan jihar ciki har da Gwamna Soludo.

By Babaji