
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Asabar Majalisar Ƙolin Shari’a a Nijeriya (SCSN) ta kirayi Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta soke naɗin da ya yi wa sabon Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan.
Hakan na zuwa ne bayan da jaridar ShaharaReporters ta fitar da wani rahoto da ke bayyana yadda Farfesa Amupitan ya taɓa yin wani rubutun shari’a da ke zargin yadda ake yi wa al’ummar Kiristoci da wasu ƙabilu kisan mummuƙe sakamakon yawan kai musu hare-hare a sassan Nijeriya.
A kwanan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin jagoran INEC, wanda ya yi wa rubutun nasa laƙabi da “Legal Brief: Genocide in Nigeria – The Implications for the International Community.”
Kwamitin ci-gaban ƴancin al’umma da na addini na ƙasa-da-ƙasa a Nijeriya (ICON) da ke da ofisoshi a Jos da Abuja shi ya wallafa rubutun, kamar yadda ShaharaReporters ta ruwaito.
Majalisar Ƙolin Shari’ar ta bayyana saƙon a matsayin abin fusatarwa da ka iya haddasa tarzoma musamman duba da yadda hakan ke nuni da adawa da al’ummar Musulumi a arewacin Nijeriya.
A wata takarda da ta fitar a ranar Juma’a, SCSN ta nuna kaɗuwarta bisa binciken ShaharaReporters na zargin da Amupitan ya yi akan arewa cewa ana kiran Kiristoci a arewa da kuma alaƙanta rashin tsaro da Jihadin Shehu Uthman Ɗan Fodiyo da aka yi a ƙarni na 19.
Majalisar ta bayyana matsayar Farfesan a matsayin barazana ga harkokin al’umma musamman kasancewar ofishin da Shugaban ƙasa ya ba shi na ya jagoranta, shi ke kula da martabar dimukraɗiyyar ƙasar.
Ta kuma bayyana ikirarin a matsayin abinda ka iya haddasa rarrabuwar kai, cin fuska da faɗin rashin gaskiya akan haƙiƙanin abinda aka san al’umma mafi rinjaye da shi a ƙasar.
