Zauren shugabannin hukumomin gwamnatin Kano sun yarjewa Abba sake tsayawa takarar gwamna

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban zauren Tukur Bala ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina wanda ɗaukacin shugabannin hukumomin suka halarta.

Tukur Bala wanda babban daraktan hukumar yawon buɗe ido na jihar Kano ya ce cigaba da aka samu a tsawon mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano yasa suka ga wajibi ne su kira wannan taron su nuna goyon bayan su ga Abba domin ya sake tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar.

Tukur ya ce da hawan gwamna Abba Yusuf mulkin ya kafa dokar ta ɓaci kan harkar ilimi a jihar.

“Wanda sakamakon haka jihar Kano ta zo ta ɗaya a sakamakon jarabawar NECO,ya kuma samar da kayayyakin koyar wa a makarantun firamare da na sakandare a faɗin jihar,”Inji shugaban zauren.

Haka kuma duk malamin makaranta da ya cancanci karin girma Abba yayi masa ba tare da ya tsallake kowa ba acewar Tukur Bala.

Ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir ya gaji bashi na Naira biliyan 41 da yan fasho suke bi na tsawon shekaru 8 amma ya zuwa yanzu ya biya su Naira biliyan 27 “sauran ma nan bada jimawa ba zai kammala biyan yan fansho kuɗaɗen su na ajiye aiki.

Ɓangaran samar da hasken wutar lantarki kuwa, Tukur ya ce yanzu haka tashar wutar lantarki na Tiga na samar da mega watt 10,sai na chalawa da aikin samar da wutar lantarki ya kai 75 bisa 100 inji shugaban zauren.

Gwamnatin Abba Kabir ta kuma tallafawa mata marasa ƙarfi su dubu 36 da tallafi na Naira dubu 50 kowanne da sauran irin waɗannan aiki masu ɗinbin yawa.

“Ganin waɗannan ayyuka da kuma nuna tausayi da jin ƙai da yake nuna wannan wannan zauren na shugabannin hukumomi na gwamnatin Kano muka ga zama wajibi mu kira wannan taron domin mu aminta da Abba ya sake tsayawa takarar kujerar Gwamnan jihar kano,”inji Tukur Bala.

Ya ce zauren Shugabannin za su yi duk abu mai yiwuwa wajen taimaka a cimma wannan buri na su ya ce.

Shugabannin hukumomin sun kuma jaddada cikakken mubaya’a ga jagora Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Shugabannin hukumomin na Katsina na halartar taron sanin makaman aiki na kwanaki biyu.

By ukarofi