‘Yana da haɗari’: Miyetti Allah ta gargaɗi Amurka akan hukunta ƴaƴanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Makiyayan Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN), ta yi tir da matakin ƴan majalisar Amurka na a hukunta ta bisa zargin ta da tauye ƴancin addini a Nijeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar Wakilan Amurka ta yi kira ga ma’aikatun tsaro da asusun ƙasar ta hukunta wasu ƙungiyoyin Nijeriya ciki har da Miyetti Allah na Makiyaya da Miyetti Allah Kautal Hore.

Da fari Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta bisa zargin musguna wa Kiristoci.

A wata hira da jaridar Daily Post, jagoran Miyetti Allah, Abdullahi Bakoji Adamu, ya ce ba daidai ba ne Amurka ta yi amfani da binciken da ba a kammala ba wajen ɗaukar mataki.

Bakoji, wanda shi ne Daraktan Hukumar Ƴancin Ɗan-adam ta ƙasa-da-ƙasa a Nijeriya, ya bayyan cewa babu adalci a ɗauki mataki akan baki ɗaya ƴaƴan ƙungiyar akan abinda ake zargin tsiraru daga cikin su ke aikatawa.

Ya kuma ce, yana da haɗari a ɗauki mataki ba tare da yin binciken da ya dace ba akan al’amarin, saboda matuƙar aka samu mutum da hannu a taka doka, sai an bincike shi sannan a hukunta shi ba wai duka ɓangaren ba, lamarin da ka iya shafar waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ƙara da cewa, ɗaukar matakin kan mai uwa-da-wabi zai haifar fargaba da kuskuren fahimta acikin al’ummar Fulani da kuma ƙara haddasa taɓarɓarewar tsaro.

Har’ilayau, tsohon sojan ya ce akwai buƙatar gwamnatocin ƙasashen wajen su haɗa hannu da Nijeriya akan lamuran tsaro a madadin yin barazana.

By Babaji