Ɗalibai 17,000 suka amfana da tallafin Gidauniyar Lado Ɗanmarke

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sakataren Gidauniyar Muhammad Ghali Bakori ya shaidawa manema labarai a cikin jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma wajen da Gidauniyar ta gama tantance ɗalibai 1,500 da za biya masu kuɗin makaranta.

Ya ce Gidauniyar ta zaɓo ɗaliban waɗanda yan asalin jihar Katsina ne daga manyan makarantu na jihar da ma na wasu jihohi domin biya masu kuɗin makaranta.

“Makarantun sun haɗa da jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma da jami’ar Umaru Musa Yar’adua da kuma makarantar kimiya da fasaha na Hassan Usman da sauran su,”Ghali ya ce.

Ya ƙara da cewa akwai jami’ar ABU Zaria da ta Usman Danfodiyo a Sokoto dukkan su ɗalibai yan asalin jihar sun amfani da tallafin Ɗan marke.

Sakataren Gidauniyar ya bayyana cewa ba su tsaya anan ba , Gidauniyar ta tallafawa harkar kiwon lafiya da taimakawa mata masu ƙananan sana’o’i.

Ghali ya ce a kowace ƙaramar hukuma na jihar Katsina, Gidauniyar ta ɗauki asibitoci uku da ta taimakawa marasa lafiya da magani,” har suma masu jinyar marasa lafiya an tallafa masu inji Sakataren Gidauniyar.

Ya kuma nuna cewa Gidauniyar ba ta nuna bambancin siyasa, matukar ɗalibi ya cancanci tallafi sai ya ba da numbar da za a buɗe shafin makarantar da za a biya masa kuɗin makaranta.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafi Zainab Yahuza da ke da lalurar ƙafa ta nuna jin daɗin ta da har ta samu aka biya mata kuɗin makaranta.

Ta ce su masu buƙata na musamman da suka sami kansu cikin wannan hali bai sa tayi bara ba,taga zata iya karatu kuma ba duka ne zasu iya biyan kuɗin makarba.

Sai tayi godiya ga Gidauniyar Lado Ɗanmarke bisa irin wannan taimako ga dalibai musamman masu lalura ta musamman.

By ukarofi