Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun mamaye Majalisar Dokokin Filato

Jami’an ‘yan sada dauke da bindigogi a ranar Talata, sun karbe Majalisar Dokokin Jihar Filato tare da hana wasu tsigaggun mambobin majalisar shiga harabar majalisar.

Rahotanni sun ce an ga yadda ‘yan sanda suka buɗe tsigaggun mambobin majalisar su 16 na Jam’iyyar PDP da barkonon-tsohuwa.

MANHAJA ta kalato wannan yamutsin ya afku ne a lokacin da tsigaggun ‘yan majalisar tare da magoya bayansu suka isa tsohuwar Fadar Gwamnatin jihar da ke Rayfield a Jos don shirin komawa bakin aikin.

Rahoto ya ce ‘yan sanda da takwarorinsu sun mamaye harabar Fadar Gwamnatin inda suka hana tsigaggun ‘yan mambobin shiga majalisar.

Sai a nasu bangaren , ‘yan majalisar sun lashi takobin babu gudu, ba ja da baya.