Da ina da iko da cikin mako biyu zan magance matsalar tsaron Zamfara – Gwamna Lawal

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce da a ce yana da cikakken iko da jami’an tsaro, da zai iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar shi a cikin mako biyu.

Gwamnan ya kuma ce ya san dukkan inda ’yan bindigar jihar suke buya.

Da yake jawabi a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, gwamnan ya ce babban ƙalubalen shi a yaki da ’yan bindiga a jihar shi ne rashin cikakken iko da jami’an tsaro.

Ya ce shugabannin rundunonin tsaron da ke jihar suna karɓar umarni ne kawai daga hedkwatocinsu da ke Abuja, bad aga wajen shi ba.

A cewar Gwamnan, “Na rantse da Allah na san duk inda wani shugaban ’yan bindiga yake a Zamfara, kuma duk inda ya fita ya je na sani.

“Yanzu da wayata zan iya nuna muku inda wadannan ’yan ta’addan suke a yau. Amma babu abin da za mu iya yi musu.

“Wallahi a yau da ina da iko da jami’an tsaro, ina mai tabbatar maka za mu iya kawo karshen ’yan bindiga a Zamfara cikin wata biyu.

“A lokuta da dama nakan zubar da hawaye ga mutanena ganin yadda matsalar take, amma ba ni da ikon da zan ba jami’an tsaro umarni su yi maganinta.

“Akwai lokacin da ’yan ta’adda suka taba kai hari karamar hukumar Shinkafi, kuma ina zaune a nan lokacin da aka ankarar da jami’an tsaro, amma suka ki zuwa saboda wai ba a ba su umarni daga Abuja ba. Wannan ce babbar matsalar da muka fuskanta, amma mun dogara ga Allah, zai kawo mana mafita.”

Gwamna Lawal ya ce amma duk da haka, gwamnatin jihar na ba jami’an tsaro tallafin kayan aiki da kuɗaɗen gudanarwa na yau da kullum, inda ya ce bayanan hakan na nan ga duk mai buƙata.

Ya kuma ce ko a wata biyu da suka gabata, gwamnatin jihar ta raba motocin sintiri guda 150 ga jami’an tsaro na sojoji, ’yan sanda da DSS da kuma sibil difens domin su inganta ayyukansu.

Gwamnan ya kuma ce ya ɗauko hayar mafarauta sama da 2,000 daga jihohin Borno da Yobe zuwa jihar domin tallafa wa ƙoƙarin jihar na yaƙi da ’yan fashin dajin.

By ukarofi