Da Kwankwaso na kishin Arewa da ya janye wa Atiku Abubakar takara!

Daga MUHAMMAD SHAMSUDDEEN (Phd)

Wannan furuci shi ne yake ta kewaya a tsakanin al’umma, musamman na Arewacin Nijeriya, daga vangarori daban-daban na jama’a. Kama daga Malamai, jagorori, ‘yan siyasa, ‘yan Boko, da ma ragowar mutane.

Babban dalilin da masu wannan ra’ayin suke kawowa shi ne, Inyamurai sun ba wa Peter Obi takara, haka nan Yarabawa sun yarjewa Bola Ahmed Tinubu ya yi takara daga yankinsu shi kaɗai, amma shi Kwankwaso ya ki ya janye wa Atiku.

Ƙananan dalilai kuma sun haɗa da cewa, Kwankwaso ‘Local Champion’ ne, ba zai iya cin zave ba, wasu kuma su ce Tinubu yake yi wa aiki. Bisa wannan ne nake so na yi tsokaci a kai.

Da farko, shi kansa babban dalilin da ake bayarwa na cewa Inyamurai da Yarabawa sun tsayar da ‘yan takara ɗai-ɗai ne to ba gaskiya ba ne. Misali, dukkanninmu ‘yan Nigeria mun san yadda aka fafata a lokacin zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC mai tsintsiya, da kuma PDP mai lema; shin Inyamurai sun janye wa junansu? Ko kuwa Yarabawa ne suka zavo Tinubu?

A taƙaice, Mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osibanjo, shi ne wanda ya fi dagewa a takararsa, duk da kusancinsa da Tinubu, har sai lokacin da Gwabnonin Arewa suka yi jan-ido, suka ƙwato wa Tinubun takara da ƙarfin tsiya. Wannan abu ne sananne ba na buƙatar dogon bayani. Haka ma ta faru a PDP; shin Gwamna Bala Mohammed ya janye wa Atiku, ko kuwa Olivia Diana ta janye wa Pius Anyim?

Shi kansa Peter Obi uwar bari ya gani ya gudu daga PDPn ya je ya dauko Labour Party, me ya sa bai janyewa Pius Anyim ba? Amma ba wanda ya ce ba sa kishin yankinsu sai Kwankwaso kaɗai? Wannan tsagwaron rashin adalci ne.

Wataƙila wasu su ce ai wannan zaɓen fidda gwani ne, kamata ya yi yanzu Kwankwaso ya janye tun da an zo matakin ƙarshe. Wannan ma babban kuskure ne, domin kuwa ba Tinubu ne kaɗai bayarabe da yake takara ba a yanzun ma; Abiola Kolawale Yana takara a PRP, Omoyele Sowore Yana takara a AAC, ga Oluwafemi Adenuga a Boot Party, da wasu ma da ban faɗa ba, Kuma dukkansu Yarabawa ne.

Haka nan daga ɓangaren Inyamurai, bayan shi Peter Obi, akwai Osita Nnadi a APP, sannan ga Chukwudi Umeadi na APGA, ga kuma Daberechukwu Nwanyanwu na ZLP; duk waɗannan Inyamurai ne. Kuma ko da a Arewa, akwai Matashi Ado-Ibrahim Abdulmalik na YPP, akwai Mamman Ɗantalle na APM, ga kuma Yabagi Sani na ADP. Duk waɗannan su ma rashin kishin yankinsu ne ya sa suke takara? Menene ya sa Kwankwaso kaɗai za a nemi janyewarsa? Wannan wane irin tunani ne?

Malamai da suke maganar addini, su sani ko da Kwankwaso ya janye wa Atiku saboda musulunci, to akwai wasu ‘yan takarar musulmai aƙalla su biyar. To yaya za a yi da su? Ko Kwankwaso ne kawai Musulmi?

A taƙaice ma, Bola Ahmed Tinubu da shi da mataimakinsa Kashim Shettima dukkansu Musulmai ne. Kenan idan wannan tunanin ne, sai Atiku ya janye wa Tinubu tun da shi da mataimakinsa duk Musulmai ne. Ko kuwa musuluncin Atiku ya fi na Tinubu? Ya kamata mu ji tsoron Allah!

Kuma ko a tarihin Musulunci, babu wani lokaci da aka taba samun Shugabancin da babu hamayya, tun daga kan Khalifah na farko, Sayyadi Abubakar (R.A). Haka idan ka biyo tarihi, har zuwa sauran ƙasashen Musulmi na zamanin nan. Hatta waɗanda suke tsarin Mulukiyya irinsu Saudi Arabia, akan samu ‘yan adawa, ko kuma masu neman mulkin ya dawo hannunsu duk lokacin da wani Sarki ya mutu za a naɗa wani, ballantana a ƙarƙashin tsarin demokradiyya. Kuma babu Wanda yake zarginsu da rashin kishin musulunci, sai Kwankwaso?

Idan Kuma batun kishin Arewa ne, don Allah ka tambayi kanka, tsakanin Atiku da Kwankwaso wanene a zahiri yake kishin Arewa? Wannan maganar mun Sha tattauna ta babu buƙatar sake maimaitawa, saboda dalilan a fili suke. Kowa ya yi wa kansa alƙalanci.

Batun ‘local champion’ ko Kuma Kwankwaso ba zai iya cin zaɓe ba, wannan lokaci ne zai yi alƙalanci. Ita dama kyawun dimokwaraɗiyya kenan, kowa ya fito ya gwada farin jininsa, wanda duk Allah ya ba wa sa’a, jama’a suka zaɓe shi, shikenan babu wani tashin hankali; “ku yi ta kanku mu ma mu yi ta kanmu”, kamar yadda Ado Gwanja yake faɗa.

Waɗanda suke ganin Kwankwaso Tinubu yake yi wa takara kuma, wannan yaudarar kai ne. To idan Kwankwaso ya janye wa Tinubu takara ita jam’iyyarsa ta NNPP da sauran ‘yan takarkaru a matakai daban-daban a duk jihohin Nijeriya, ya zai yi da su? A ce duk aikin da bawan Allan nan yake yi, da yawon buɗe ofisoshin Jam’iyya a faɗin Nijeriya a ce duk wani yake yiwa aiki? To nawa ya ba shi da zai yi masa wannan aikin?

Wannan aikin da Kwankwaso yake yi ko Mataimakin Shugaban ƙasa Tinubu zai ba shi idan ya ci zaɓe ai ba zai iya biyansa ba. Duk mai hankali ya San cewar takarar Kwankwaso ta gaskiya ce, Kuma ya himmatu wajen ganin ya samu nasara a zaɓe Mai zuwa, tare da duk masu goya masa baya. Idan Kuma kana ganin wani yake wa aiki to ai lokaci alkali ne.

Muhammad Shamsuddeen, PhD ya rubuto daga Jami’ar Bayero, Kano.
Lambar waya: 08181000300

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *